Rashin tsaro: Hon. Umaru Bago ya yi Allah-wadai da rawar Shugaba Buhari

Rashin tsaro: Hon. Umaru Bago ya yi Allah-wadai da rawar Shugaba Buhari

- Mohammed Umar Bago ya yarda gazawar Buhari a kan tsaro ta fito fili

- Bago ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi maganin miyagun 'yan bindiga

- ‘Dan Majalisar ya ce ba a fadawa Buhari gaskiya, ko ya yi kunnen-kashi

Hon. Mohammed Umar Bago ya yi magana bayan ‘yan majalisar wakilai sun yi wani zama da sufetan ‘yan sandan Najeriya a kan sha’anin tsaro.

Mohammed Umar Bago mai wakiltar Chanchaga ya zanta da RfI Hausa inda ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza.

“Alal-hakika an yi daidai idan aka ce mun yi shiru, domin gwamnatinmu na APC ta kasa a kan maganar tsaro.” Inji ‘dan majalisar na jam’iyyar APC.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun bukaci N270m kafin su saki Daliban ABU Zaria

Umar Bago ya kara da cewa: “Abin da ya sa shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari bai samu masu fada masa gaskiya ba, ko kuma ya na ji, ya ki ya ji.”

‘Dan siyasar ya ce ganin yadda aka bar ‘yan bindiga suna cin karensu babu babbaka, amma aka shawo kan #EndSARS, ya nuna ba da gaske ake yi ba.

“Yau mako daya kenan kullum sai an tare mutane a hanyar Abuja. Yanzu ace ba za a fito da sojoji da ‘yan sanda a shiga dajin nan a kai sa kasa baki daya ba?”

A cewar Hon. Bago, tsefe dajin Kaduna zuwa Abuja bai fi karfin jami’an tsaron Najeriya ba, amma an gagara yi, ya bada shawarar a ba sha’anin tsaro karfi.

KU KARANTA: Jigon APC ya na sha’awar zuba kudi domin farfado da Arsenal

Rashin tsaro: Hon. Umaru Bago ya yi Allah-wadai da rawar Shugaba Buhari
Buhari a Aso Villa Hoto: www.rfi.fr/ha/najeriya
Asali: UGC

“Mu je wasu kasashe mu nemo wadanda za su taya mu (yaki), amma mu na kallo a zo har gidajenmu a yankamu, wannan abin fa ba abu mai kyau ba ne.”

“Siyasa ai riga ce, idan ka ga dam aka cire jam’iyya. Maganar ‘Dan Najeriya ake yi.” Ya ce: “Mu na kallo, ba ka iya kwanciya a gidanka, ni daga Neja na ke.”

Ya ce ana kallon miyagu suna yawo kan babura da bindigogi amma babu abin da aka yi. Bago ya ce laifin ba na IGP ba ne, matsalar ta na kan shugaban kasa.

A makon nan kuma ku ka ji cewa miyagun nan da ake magana sun kashe wani Mai Gari da ‘Dansa a Kaduna, an harbe Mai dakinsa a Zangon-Kataf, Kaduna.

An kai hari cikin tsakar dare ne, inda aka kashe Mai Garin bayan an harbe matarsa da 'yarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng