Wata sabuwa: IGP ya buƙaci N24.8bn domin sayen fetur wa motoci da baburan ƴan sanda
- IGP Mohammed Adamu ya ce rundunar na bukatar akalla biliyan 24.8 duk shekara domin zuba wa ababen hawansu mai
- Adamu ya bayyana hakan ne lokacin da yake kare kasafin kudin hukumar na 2021 a gaban kwamitin majalisar wakilai
- Ya ce an zaftare kasafin kudin da aka ware masu na 2021 zuwa biliyan 449.6 daga naira biliyan 469.4
Sufeto janar na yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bayyana cewa rundunar za ta bukaci naira biliyan 24.8 domin zuba wa ababen hawanta mai a duk shekara.
Shugaban yan sandan ya bayyana hakan ne a yayin kare kasafin kudin 2021 a gaban kwamitin yan sanda na majalisar wakilai.
KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Satar al'aurar mutane ta yawaita a Benue, an sanya dokar ta ɓaci
Ya bayyana cewa suna fuskantar tarnaki sakamakon rashin kebe masu isashen kaso a kasafin kudi. shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
Adamu ya ce:
“Babbar matsalar ita ce abinda aka ware mana ba zai ishe mu gudanar da ayyukan mu tsawon shekara guda ba.
“Idan ka dauki misali, man fetur da ababen hawanmu ke sha a kulla-yaumin, motocinmu kan sha mai na kimanin naira biliyan 22.5 a cikin shekara kawai.
“Idan ka hada lissafin, a man fetur kawai an kusan karar da abinda aka ware mana, ba a ma zo ga bangaren gyare-gyare ba. Idan muna son kula da ababen hawanmu, muna bukatar akalla sama da naira biliyan takwas a shekara daya."
KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: Sabuwar cuta ta ɓulla a Nigeria, ta kashe 17 a Benue
Shugaban yan sandan ya ce a kudin da aka ware musu a kasafin 2021 na Naira biliyan 469.4 an zaftare shi zuwa Naira biliyan 449.6.
A wani labarin kuma, hukumar 'yan sanda ta jihar Legas ta bayyana korar jami'an 'yan sanda guda 10 a ranar Laraba da tayi, saboda sun aikata laifuka daban-daban.
Kakakin hukumar, SP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a wata takarda da ya sa hannu, kuma ya gabatar wa manema labarai a jihar Legas.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng