An sallami 'yan sanda 10 daga aiki a jihar Legas

An sallami 'yan sanda 10 daga aiki a jihar Legas

- Hukumar 'yan sandan jihar Legas ta kori jami'anta guda 10 saboda aikata laifuka daban-daban

- Laifukan da suka aikata sun hada da karbar rashawa, amfani da matsayinsu wurin yin zalunci da sauransu

- Kakakin hukumar, SP Olumuyiwa Adejobi, ya sanar da hakan a wata takarda da ya saka hannu ranar Laraba

Hukumar 'yan sanda ta jihar Legas ta bayyana korar jami'an 'yan sanda guda 10 a ranar Laraba da tayi, saboda sun aikata laifuka daban-daban.

Kakakin hukumar, SP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a wata takarda da ya sa hannu, kuma ya gabatar wa manema labarai a jihar Legas.

Kamar yadda kakakin yace, anyi korar ne don ladabtar da 'yan sandar jihar, Daily Nigerian ta wallafa.

KU KARANTA: Wanda ya hada bidiyon auren Buhari da Sadiya ya gurfana a gaban kotu

Adejobi ya ce hukumar ta binciki 'yan sanda 81 da suka yi laifuka daban-daban, tsakanin watan Oktoban 2019 zuwa watan Oktoban 2020.

A cewarsa, laifukan sun hada da kisa, amfani da matsayinsu su yi zalunci, rashawa da kuma rashin bin dokokin aikin.

An sallami 'yan sanda 10 daga aiki a jihar Legas
An sallami 'yan sanda 10 daga aiki a jihar Legas. Hoto daga @daily_Nigerian
Asali: UGC

Ya kara da cewa, hukumar ta kori jami'ai 10, ta rage matsayin 18 sannan ta bai wa sauran wasikun jan kunne.

Ya shawarci jama'a da su tabbatar sun kai karar duk wani laifi da suka ga 'yan sandan sun yi, don hakan ne kadai zai kawo gyara a kasar nan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga na sanya mana haraji kafin su bar mu girbin abinda muka noma, Manoma

A wani labari na daban, rundunar sojoji ta kashe wata mata mai dauke da abu mai fashewa da wasu 'yan bindiga 7 a Borno da jihar Yobe, The Punch ta wallafa.

Matar, tayi yunkurin fasa abun a sansanin sojoji na 7 da ke Bama, jihar Borno, a ranar 3 ga watan Nuwamba, amma rundunar suka yi gaggawar kashe ta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel