Babbar magana: Satar al'aurar mutane ta yawaita a Benue, an sanya dokar ta ɓaci

Babbar magana: Satar al'aurar mutane ta yawaita a Benue, an sanya dokar ta ɓaci

- An sanya dokar ta baci a garin Daudu da ke karamar hukumar Guma, jihar Benue kan zargin satar al’aurar mutane da ya yawaita a yankin

- Matasa a yankin dai sun tayar da zanga-zanga inda suke zargin wasu mutane da sacewa mutane maza da mata al'aurarsu

- Shugaban karamar hukumar, Caleb Aba, ya ce an sanya dokar kullen ne domin yi wa tufkar hanci tun wurwuri

Shugaban karamar hukumar Guma da ke jihar Benue, Caleb Aba, ya sanya dokar kulle na sa’o’i 12 a garin Daudu kan zargin satar al’aurar mutane da ya yawaita a yankin.

Garin Daudu wanda ke a hanyar babbar titin Makurdi-Lafia ya fuskanci tashin hankalin daga matasa kan zargin satar al’aurar mutane da ake zargin wasu mazaje da yi.

Shugaban karamar hukumar Guma ya fada ma manema labarai a Makurdi a jiya Laraba cewa dokar kullen, wacce ta fara a ranar Talata, zai kasance tsakanin 8pm da 6am har sai lamarin tsaro ya inganta.

Ya bayyana cewa an yanke hukuncin sanya dokar ta baci ne saboda fargabar da matasa ke haddasawa, inda ya kara da cewa duk da shugabannin garin da Gwamna Samuel Ortom sun shiga lamarin, matasan sun ci gaba da yada zargin satar al’aurar.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Jerin sunayen yan Najeriya 50 da aka gurfanar a gaban kotu kan zanga zangar

Babbar magana: Satar al'aurar mutane ta yawaita a Benue, an sanya dokar ta ɓaci
Babbar magana: Satar al'aurar mutane ta yawaita a Benue, an sanya dokar ta ɓaci Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Aba ya ce matasan a ranar Litinin, sun kai mamaya ofishin yan sanda a garin sannan suka yi yunkurin taba shi kan sabon zargin batar al’aura, jaridar The Nation ta ruwaito.

“Dalilin da yasa muka sanya dokar ta baci shine cewa matasa a garin Daudu sun koka sannan suka zargi wasu mutane da cire masu al’aura, na maza da mata.

“Sun kona kayayyakin wadanda suke zargi sannan har suka kashe wani fasto wanda suke zargi da zama umulaba’isin abun.

“Mun roke su a kan kada su dauki doka a hannunsu. Hatta da gwamnan ya roke su.

“Amma a ranar Litinin, matasan sun tattara kansu sannan suka je ofishin yan sanda a Daudu,sun yi barazanar kona shi, inda suka zargi wani mutum da suka yi wa dukan kawo wuka da satar al’aurar wani.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Kotu ta garƙame wasu mata biyu da laifin yunƙurin kashe gwamna Oyetola

“Saboda abun ya fara yawa sannan kuma ga dukkan alamu za su yi barna idan aka barsu suna yawo kansu tsaye. Wannan ne dalilin sanya dokar kullen,” in ji Shugaban.

Ya ce an kama wani dan achaba a kan nasaba da lamarin a ranar Litinin.

A wani labarin, mun ji cewa akalla mutane 17 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta a garin Okpeilo-Otukpa, karamar hukumar Ogbadilo da ke jihar Benue.

Wata sanarwa da aka saki a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba, daga kwamishinan lafiya na jihar, Dr Emmanuel Ikwulono, ya tabbatar da mace-macen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng