Ana wata ga wata: Sabuwar cuta ta ɓulla a Nigeria, ta kashe 17 a Benue

Ana wata ga wata: Sabuwar cuta ta ɓulla a Nigeria, ta kashe 17 a Benue

- Wata bakuwar cuta ta bulla a garin Okpeilo-Otukpa da ke jihar Benue

- An tattaro cewa cutar ta halaka mutane 17 cikin yan kwanaki yayinda sauran mutane da suka harbu suke samun kulawa

- Gwamnatin jihar ta tabbatar da lamarin, ta bayyana cewa an fara bincike a kan cutar

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 17 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta a garin Okpeilo-Otukpa, karamar hukumar Ogbadilo da ke jihar Benue.

Wata sanarwa da aka saki a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba, daga kwamishinan lafiya na jihar, Dr Emmanuel Ikwulono, ya tabbatar da mace-macen, jaridar ThisDay ta ruwaito.

Ya kara da cewa sauran wadanda suka harbu da cutar na samun kulawar likitoci a asibitoci daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Kotu ta garƙame wasu mata biyu da laifin yunƙurin kashe gwamna Oyetola

Ana wata ga wata: Sabuwar cuta ta ɓulla a Nigeria, ta kashe 17 a Benue
Ana wata ga wata: Sabuwar cuta ta ɓulla a Nigeria, ta kashe 17 a Benue Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati na sane da barkewar cutar sannan kuma ta kafa bincike domin gano musababbin cutar.

Ikulono ya kara da cewa Gwamna Samuel Ortom ya amince da kudade domin gudanar da binciken da ya kamata.

A wani lamari mai ban al'ajabi, mun ji cewa Kwamishinan lafiya na jihar Benue, Dr Emmanuel Ikwulono, ya rasu.

KU KARANTA KUMA: Jihar Kaduna na alfahari da Balarabe Musa – Elrufai

A ranar 5 ga watan Agustan 2020 ne aka rantsar da Dr Ikwulono a matsayin kwamishinan lafiya da harkokin jama’a na jihar Benue.

Ya maye gurbin Dr Sunday Ongbabo wanda ya yi murabus daga majalisar zartarwa ta jihar.

Wata majiya ta gidan gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa kwamishinan wanda aka ba gado a asibiti ya mutu sakamakon rashin nasara da aka samu a aikin tiyata da aka yi masa na wani ciwo da ba a bayyana ba.

“Ya halarci zaman majalisar zartarwar jihar da aka gudnar na karshe a makon da ya gabata sannan ya je aka yi masa aiki.

“Mutuwarsa ya zo kamar almara a yammacin nan,” in ji majiyar gwamnatin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel