Hatsarin Mota Ya Rutsa da Fitaccen Dan Wasan Kwallon Najeriya a Jamus
- Tauraron Bayer Leverkusen, Victor Boniface ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a safiyar Lahadi
- Dan asalin Najeriya, Boniface ya wallafa bidiyon yadda motarsa ta yi raga raga tare da dora hoton hannunsa da ke zubar da jini
- Victor Boniface ya yi hatsarin ne kasa da awanni 24 da cin kwallo a wasan kungiyarsa da Eintracht Frankfurt a gasar Bundesliga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jamus - Dan wasan Najeriya Victor Boniface ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a kasar Jamus.
Dan wasan wanda ke taka leda a kungiyar Bayer Leverkusen ta Jamus, ya wallafa hoton motarsa da ta yi raga-raga a ranar Lahadi.
Dan wasan Najeriya ya yi hatsari
Victor Boniface ya yi hatsarin ne kasa da awanni 24 da buga wasa tsakanin kungiyarsa da Eintracht Frankfurt a gasar cin kofin Bundesliga, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Bayer Leverkusen ta lallasa Eintracht Frankfurt da ci 2 da 1 a filin wasa na BayArena bayan Boniface ya zura kwallo daya.
An garzaya da Boniface Asibiti
Jaridar Daily Mail ta rahoto cewa an garzaya da dan wasan asibiti bayan hatsarin, inda daga bisani ya wallafa hotonsa yana kwance a gadon asibiti.
An ce ya samu kananan raunuka biyu a hannu. Babu cikakkun bayanai game da halin da direban ko fasinjojin motar da suka yi karon tare suke ciki.
An ce Boniface a cikin wata mota kirar Mercedes da ke hanyarsa ta daukar abokansa a filin jirgin sama na Frankfurt, ya yi hatsari da wata babbar mota a safiyar Lahadi.
Bidiyon Boniface bayan hatsarin mota
Wani faifan bidiyon ya nuna daya daga cikin hannayen Boniface yana zubar da jini bayan hadarin motar.
A cikin faifan bidiyon, an ga motar mai launin baki ta yi raga raga a gefen dama, yayin da sauran jikinta ya lokame.
"Ubangiji ne mai yin yadda ya so," a cewar Boniface a lokacin da ya wallafa bidiyon.
Tsohon dan wasan Eagles ya yi hatsari
A wani labarin, mun rahoto cewa tsohon ɗan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya gamu da hatsarin mota a a kan hanyarsa ta zuwa Abuja tare da kaninsa da matarsa.
An rahoto cewa hatsarin ya yi silar mutuwar kanin Tijjani Babangida mai suna Ibrahim Babangida wanda shi ma tsohon dan wasan Eagles ne.
Asali: Legit.ng