Tijjani Babangida Ya Rasa Ɗansa Yayin da Matarsa, Maryam Waziri Ke Cikin Wani Yanayi

Tijjani Babangida Ya Rasa Ɗansa Yayin da Matarsa, Maryam Waziri Ke Cikin Wani Yanayi

  • An shiga jimami bayan rasuwar yaron tsohon dan wasan Najeriya, Tijjani Babangida bayan hatsarin mota
  • Yaron wanda bai wuce shekara daya ba ya rasu ne a yau Asabar 11 ga watan Mayu a asibiti bayan hatsarin mota a Kaduna
  • Yayin hatsarin da ya afku, Tijjani Babangida ya rasa kaninsa na jini mai suna Ibrahim Babangida nan take

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohuwar jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Waziri ta gamu da hatsarin mota a jihar Kaduna yayin da ta rasa ɗanta.

An sanar da cewa Maryam ta rasa wasu ɓangarori na jikinta musamman a fuska da suka haɗa da ido da kuma kunne.

Kara karanta wannan

Manyan Janar 29 sun yi ritaya daga gidan soja ana tsaka da rashin tsaro

Maryam Waziri ta na cikin wani yanayi yayin da ɗansu ya rasu
Tijjani Babangida ya rasa ɗansa yayin da Matarsa, Maryam Waziri ke cikin wani hali. Hoto: Maryam Waziri.
Asali: Facebook

Hatsarin ya jawo rasa rai a Kaduna

Wannan na zuwa ne bayan mummunan hatsarin mota da ya afku da ita da kuma mijinta, Tijjani Babangida da kaninsa, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanadin hatsarin motar ya jawo rasa kanin mijinta mai suna Ibrahim Babangida nan take wanda tuni aka yi sallar jana'izarsa.

Bayan faruwar hatsarin, an kwashi Maryam da kuma mijinta, Tijjani Babangida zuwa asibiti domin ba su kulawa na musamman.

Bayan shafe kwanaki biyu a asibitin ne aka sanar da ɗansu mai shekara daya ya rasu bayan samun munanan raunuka a hatsarin.

Tijjani Babangida ya gamu da hatsarin mota

Kun ji cewa Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya gamu da hatsarin mota a jihar Kaduna.

Hatsarin ya faru ne a ranar Alhamis 9 ga watan Mayu a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria a jihar.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Rahotanni sun tabbatar da cewa hatsarin ya rusa da kanin fitaccen ɗan wasan mai suna Ibrahim Babangida wanda ya rasa ransa.

Sarkin Tikau ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Tikau na jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema ya riga mu gidan gaskiya.

Iyalan marigayin ne suka tabbatar da rasuwar Sarkin da yammacin ranar Jumu'a 10 ga watan Mayun 2024 a jihar Yobe.

Sarkin ya rasu ne a Asibitin kwararru da ke garin Potiskum bayan ya sha fama da rashin lafiya ta tsawon lokaci wanda ya hana shi shiga harkokin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel