Kungiyar Al-Hilal Da Ke Saudiyya Za Ta Sayi Mbappe Akan Kudi Fiye Da €300m

Kungiyar Al-Hilal Da Ke Saudiyya Za Ta Sayi Mbappe Akan Kudi Fiye Da €300m

  • Tun bayan samun matsala da hukumomin kungiyar PSG, kungiyoyi da dama ke zawarcin Kylian Mbappe
  • Mbappe ya samu matsala da kungiyar ne bayan ya ki amincewa ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar
  • PSG ta cire sunansa a jerin 'yan wasan da za su tafi Gabas ta Tsakiya don buga wasannin share fagen kakar bana

Paris - Kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal da ke Saudiyya ta mika fiye da Yuro miliyan 300 don siyan shahararren dan kwallon kafa ta PSG, Kylian Mbappe, rahotanni sun ce PSG ta amince da tayin.

Mbappe dai na takun saka da kungiyarsa ta PSG bayan bayyana musu cewar ba zai tsawaita kwantiraginsa ba da zai kare a 2024.

Al-Hilal Da Ke Saudiyya Za Ta Sayi Mbappe Akan Kudi Fiye Da €300m
Kungiyar Al-Hilal Da Ke Saudiyya Ta Mika Tayin Kudi Fiye Da €300m Don Dauke Mbappe Daga PSG. Hoto: JULIEN DE ROSA / AFP.
Asali: AFP

Tushen matsalar da ta afku tsakanin Mbappe da PSG

Mbappe ya ki tsawaita kwantiraginsa, wanda akan ya fusata kungiyar inda suka cire sunansa a jerin 'yan kwallon da za su tafi Gabas ta Tsakiya don buga wasannin share fagen kakar bana, cewar gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Tana Dafa Taliya Da Lemun Mirinda Da Sukari Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani, kungiyar ta sa Mbappe a kasuwa inda ake rade-radin cewa zai koma Real Madrid da buga tambola, kamar yadda dan jarida, Fabrizio Romano ya tabbatar a shafinsa na Twitter.

Bayan Al-Hilal akwai kungiyoyi da ke zawarcin Mbappe kamar su Arsenal da Barcelona da Manchester United da ke son dauko dan wasan.

Sai dai har yanzu ba a ji komai daga dan wasan ko kuma wakilansa ba akan wannan ciniki da ake shirin kullawa.

Garabasar da Mbappe zai kwashe a Al-Hilal ta Saudiyya

Al-Hilal na son dauko Mbappe bayan wasu 'yan wasa daga gasar Premier sun koma buga tambola a kungiyar da ke da arziki.

Mbappe zai samu £893,000 a ko wane mako, yayin da shekara daya zai kwashi makudan kudade har £80m.

Har ila yau, dan wasan zai samu alawus da ya kai £100m, Soccernet.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Babban Jagora a Kasar Yarabawa Ya Caccaki Tinubu Kan Wahalhalun Da Ake Sha a Najeriya

Tun bayan sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da Christiano Ronaldo ya yi, 'yan wasa da dama ke kokarin komawa Saudiyya don kwashe kudade masu tsoka.

Da Alamu Messi Zai Koma Wasa A Saudi A Cinikin Da Zai Girgiza Duniyar Kwallo

A wani labarin, akwai alamu Lionel Messi zai iya komawa kasar Saudiyya da buga kwallon kafa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa dan wasan gaban na kasar Argentina zai raba gari da PSG, bayan alakarsu ta tabarbare a 'yan kwanakin nan.

Kungiyar Al-Hilal ta yi wa Messi tayin Yuro miliyan 522 duk da cewa babu tabbas hakan zai kasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.