“Menene Wannan?” Budurwa Ta Dafa Taliyarta Da Lemun Mirinda da Sukari a Bidiyo

“Menene Wannan?” Budurwa Ta Dafa Taliyarta Da Lemun Mirinda da Sukari a Bidiyo

  • Masu amfani da soshiyal midiya sun caccaki wata yar Najeriya kan wani bidiyonta tana dafa taliya da lemun kwalba
  • Bayan ta yi amfani da Mirinda, budurwar ta kuma kara sukari a cikin abinci, cewa zai kara masa dandano
  • Wasu mutane sun caccaketa kan yadda take neman suna ta hanyar girka kwamacala, wasu kuma suna ganin bata da lafiyar kwakwalwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiya yar Najeriya, Cyndy ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta baje kolin taliyar da ta dafa inda ta yi amfani da lemun Mirinda da Sukari.

Cyndy, mai nishadantarwa a TikTok ta baje kolin yadda ta girka taliya a cikin yar tukunyar suya da risho mai amfani da gas.

Budurwa ta dafa taliya da lemun kwalba
“Menene Wannan?” Budurwa Ta Dafa Taliyarta Da Lemun Mirinda da Sukari a Bidiyo Hoto: @cyndy_pek
Asali: TikTok

Ta fara da juye lemun kwalba a cikin tukunyar suya sannan ta bi sahunsa da taliya kafin ta zuba atarugu, sinadarin dandano da kuma albasa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Tuka Amala Da Na'ura Maimakon Muciya Ya Tashi Kan Yan Mata

Bayan ta gama, sai ta zuba abincin a cikin kwano sannan ta kara sukari a ciki, cewa zai kara masa dadi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon ya kare a daidai lokacin da take shirin kai abincin mai ban mamaki bakinta. Jama'a sun caccake ta kan dafa abinci da lemun kwalba.

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun caccaki budurwar

@_S I M I L A ya ce:

"Don Allah yaushe za ki yi bidiyon kashi na 2. Don Allah ki sanya lokacin da kika ziyarci bandaki a ciki."

Mimo baby ta ce:

"Nima bana son abubuwa da yawa a ciki. Kuma na kan so zuba kananzir yana sa shi dadi."

TOM ya ce:

"Duk irin abubuwa haka kamar wasa suke farawa...daga nan kafin ki sani ya zame maki jiki."

E G C money ya ce:

"Ba ku ga fuskarta ba ta kwale da yawa ta sha colos kadan."

Kara karanta wannan

“Ba Za Ki Iya Satar Amsa a Jarrabawa Ba”: Bidiyon Dalibar Jami’ar Baze Wacce Ita Kadai Ce a Ajinta

user7355988781883 ya ce:

"Don Allah saura abun goge hakora da man injin."

stars_delight ta ce:

"Biyu da safe biyu da rana sannan biyu da daddare, Allah ya baki lafiya yar'uwa."

Bidiyon wata mata tana tuka amala da na'ura ya dauka hankali

A wani labarin kuma, wata mata ta tashi kan yan mata da dama a soshiyal midiya bayan bayyanan bidiyonta tana tuka amala da na'ura maimakon muciya.

Da dama sun ce yanzu sun shirya aure domin ga dukkan alamu ba za su sha wahala ba a gidajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel