Hotuna: An Kammala Ginin Katafariyar Makarantar Boko da Ahmed Musa ya Gina, Ya Saka Mata Suna

Hotuna: An Kammala Ginin Katafariyar Makarantar Boko da Ahmed Musa ya Gina, Ya Saka Mata Suna

  • Shahararren ‘dan wasan kwallon kafa kuma kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya kammala ginin tamfatsetsiyar makarantarsa
  • Ya saka mata suna M & S International Schook inda yace yayi hakan domin karrama mahaifinsa Musa da mahaifiyarsa Sarah
  • Ya gina makarantar ne a Bukuru dake karamar hukumar Jos ta kudu a matsayin hanyar kyautatawa yankin da aka haifesa

Kyaftin din kungiyar kwallon kafan Najeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa ya gina katafariyar makaranta inda ya karanta iyayensa Musa da Sarah ta hanyar sanyawa makarantar sunayensu.

Ahmed Musa
Hotuna: An Kammala Ginin Katafariyar Makarantar Boko da Ahmed Musa ya Gina, Ya Saka Mata Suna. Hoto daga @ahmedmusa718
Asali: Instagram

Zakaran kwallon kafan wanda cikin kwanakin nan ya cika shekaru 30 a duniya ya bayyana hotunan gagarumar makarantar a ranar Lahadi a shafukansa na soshiyal midiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

2023: Dan Wani Babban Sarki Da Ya Rasu Ya Fadi Dan Takarar Da Mahaifinsa Ya So Ganin Ya Gaji Buhari

An tamfatsa ginin makarantar ne a Bukuru dake karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Kamar yadda ya bayyana, ya saka wa makarantar suna M & S International School kuma ma’anar M din Musa ne yayin da S ta kasance Sarah sunan mahaifiyarsa.

A wallafar da yayi a shafinsa na Twitter yace:

“Ina alfaharin saka mata suna bayan iyayena. Misra Musa da Mrs Sarah! M & S International School. Godiya ta tabbatar ga Allah.”

Kudi na magana: Dan kwallon Najeriya Ahmad Musa ya ginawa talakawa katafariyar makaranta a Jos

A wani labari na daban, Kaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya ci gaba da aikin gina al’umma yayin da dan wasan mai shekaru 29 ya kashe miliyoyin kudi a gina makarantar kasa da kasa a Buruku da ke garin Jos.

Ahmed Musa dai ba zai daina ba da taimako ga masu bukata, don kuwa ya gina wata makarantar zamani a garin Jos; wani yanayi na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel