2023: Dan Wani Babban Sarki Da Ya Rasu Ya Fadi Dan Takarar Da Mahaifinsa Ya So Ganin Ya Gaji Buhari

2023: Dan Wani Babban Sarki Da Ya Rasu Ya Fadi Dan Takarar Da Mahaifinsa Ya So Ganin Ya Gaji Buhari

  • Dan marigayi basaraken kasar Yarbawa, Oba Lamidi Adeyemi 111, ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC
  • Hon. Akeen Adeyemi ya bayyana burin mahaifinsa na karshe game da takarar Bola Tinubu
  • Dan autan Alaafin ya bayyana cewa burin mahaifinsa na kasrhe shine ganin tsohon gwamnan na jihar Lagas ya zama shugaban kasar Najeriya

Oyo - Dan marigayi Alaafin, Oba Lamidi Adeyemi 111, Akeem Adeyemi, ya bayyana cewa burin mahaifinsa na karshe shine ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya.

Adeyemi mai wakiltan mazabar AFIJIO/Atiba, Oyo ta gabas, Oyo ta yamma a majalisar tarayya, ya bayyana hakan ne yayin zagayowar ranar haihuwar marigayi basaraken na Oyo a karshen mako, The Nation ta rahoto.

Bola Tinubu
2023: Dan Wani Babban Sarki Da Ya Rasu Ya Fadi Dan Takarar Da Mahaifinsa Ya So Ganin Ya Gaji Buhari Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

An gudanar da bikin ne a dan karamin filin wasa da ke Ode Aremo, kusa da fadar Alaafin din.

Ya bukaci matasa da su marawa dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) baya a babban zaben kasar mai zuwa, rahoton Rivers Mirror.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan majalisar ya bayyana cewa Tinubu ya bayar da gagarumin gudunmawa wajen ci gaban kasar nan, yana mai kira ga matasa da su mayar da hankali waje daya sannan su kada kuri’unsu ga mutumin da ke da ra’ayinsu a zuciyarsa.

Ya ce:

“Muna son yin godiya gad an takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima. Wannan aiki na da muhimmanci a garemu. Yana da muhimmanci ga Oba Lamidi Adeyemi. Burinsa na karshe shine ya ga Asiwaju ya zama shuagaban kasa.
“An baiwa mutane dari biyar da ke goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima tallafin kudi a yau don su yada manufar nasarar Asiwaju Ahmed Tinubu.

“Zan yi kira ga matasa da su zuba ido sannan su mayar da hankali wajen sanin wake son su da gaskiya, wanda zai iya tallafa masu, kuma wanda ke da ra’ayin makomarsu a zuciyarsa.”

Shugaban Kasa A 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ta Bayyana Jihohin Arewa 3 Da Peter Obi Ka Iya Lashe Zabe

A gefe guda, duba ga yadda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ke kara samun farin jini, jam'iyyar APC ta yi wasu hasashe game da abubuwan da ka iya faruwa a babban zaben mai zuwa.

Mataimakiyar kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, ta bayyana cewa Obi na iya lashe wasu jihohin arewa da duk wani dan takara ke bukatar kuri'unsu don lashe zabe.

Ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da jaridar The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel