Da Dumi-Dumi: Chelsea zata barje gumi da Real Madrid da sauran wasanni uku na Kwata-Final da aka haɗa yau

Da Dumi-Dumi: Chelsea zata barje gumi da Real Madrid da sauran wasanni uku na Kwata-Final da aka haɗa yau

  • Hukumar dake shirya gasar zakarun nahiyar turai UEFA ta haɗa wasannin da za'a fafata a matakin Kwata-Final
  • Chelsea mai rike Kofin zata fafata da Real Madrid ta ƙasar Sifaniya, Man City zata ɓarje gumi da Atletico Madrid da sauran wasanni 2
  • Za'a buga wasan ƙarshe a Filin wasa na Stade de France ranar 28 ga watan Mayu, tsakanin kungiyoyi biyu da suka tsallake

Masu rike da kofin zakarun nahiyar turai, Chelsea zasu ɓarje gumi da kungiyar Sifaniya, Real Madrid, wacce ta lashe gasar sau 13 a tarihi, a wasan gab da na kusa da na ƙarshe da aka haɗa ranar Jumu'a

Daily Trust ta rahoto cewa ƙungiyar Chelsea ta na kasuwa bayan gwamnatin Burtaniya ta ƙaƙabawa mamallakin kungiyar ɗan kasar Rasha, Roman Abramovich, takunkumi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta ba da umarnin soke batun hana APC taron gangamin ranar 26 ga Maris

Burtaniya ta ƙaƙabawa Attajirin mai Chelsea takunkumi ne biyo bayan mamayar da kasarsa ta Rasha ta yi wa Ukraniya, wanda ya shiga kwanaki sama da 20.

Wasannin Kwata Final
Da Dumi-Dumi: Chelsea zata barje gumi da Real Madrid da sauran wasanni uku na Kwata-Final da aka haɗa yau Hoto: Sport Arena/Facebook
Asali: Facebook

An haɗa jadawalin wasanni hudu na Kwata-Final ranar Jumu'a a hedkwatar hukumar UEFA mai shirya gasar dake birnin Nyon, na ƙasar Switzerland.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sauran wasannin da za'a barje gumi na wannan mataki, Manchester City zata fafata da kungiyar kwallon ƙafa da Atletico Madrid.

Sauran sune, Bayern Munich zata gwabza da Villareal ta ƙasar Sifaniya, sai kuma kungiyar Benfica da zata murza leda da Liverpool ta ƙasar Ingila.

Ƙungiyoyin zasu fafata da juna a wasan farko na Kwata-Final a ranakun 5 da 6 ga watan Afrilu, yayin da wasa na biyu zai biyo baya a ranakun 12 da 13 ga watan Afrilu.

Kazalika za'a buga wasan kusa da na ƙarshe Semi-Final na farko a ranakun 26 da 27 ga watan Afrilu, yayin da za'a juya wasa na biyu a ranar 2 da kuma 4 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

'Zan cika burin yan Najeriya' Matashi dan shekara 45 ya shiga tseren gaje kujerar Buhari a 2023

Sannan kuma kungiyoyi biyu da suka samu nasarar tsallaki waɗan nan matakan za su fafata a wasan ƙarshe ranar 28 ga watan Mayu a Filin wasa na Stade de France na birnin Farisa.

Jerin wasannin Kwata-Final

Chelsea (Ingila) Vs Real Madrid (Sifaniya)

Manchester City (Ingila) Vs Atletico Madrid (Sifaniya)

Villarreal (Sifaniya) Vs Bayern Munich (Jamus)

Benfica (Fotugal) v Liverpool (Ingila)

Wasannin kusa da na karshe

Manchester City ko Atletico Madrid Vs Chelsea ko Real Madrid

Benfica ko Liverpool Vs Villarreal ko Bayern Munich

A wani labarin kuma Ko kunsan kasashen da Musulmai zasu yi dogon Azumi da kasashen da zasu yi gajere a bana Ramadan 2022?

Biliyoyin al'ummar Musulmai a faɗin duniya na gab da shiga wata mai Albarka Ramadan na shekarar 2022.

Musulman wasu ƙasashe za su fuskanci dogon Azumi na tsawon awanni a bana, yayin da wasu kuma za su yi gajere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel