Ramadan 2022: Wane kasashe ne Musulmai za su kwashe awanni da yawa da awanni kaɗan a Azumin bana

Ramadan 2022: Wane kasashe ne Musulmai za su kwashe awanni da yawa da awanni kaɗan a Azumin bana

  • Biliyoyin al'ummar Musulmai a faɗin duniya na gab da shiga wata mai Albarka Ramadan na shekarar 2022
  • Musulman wasu ƙasashe za su fuskanci dogon Azumi na tsawon awanni a bana, yayin da wasu kuma za su yi gajere
  • Haka nan akwai wasu kasashe da babu dare domin rana na faɗuwa kuma ta sake fitowa a cikin awannin da ba su zarce uku ba

Musulmai zasu fara azumin watan Ramadana a farkon watan Afrilu na wannan shekarar kuma Biliyoyin mutane ne zasu kame daga ci ko sha ko kusantar iyali na tsawon awannin rana har wata ɗaya.

Watan mai tarin ni'ima da gafarar Allah SWT, zai soma yayin da wasu sassan duniya ke cikin tsawon rana, lokacin zafi, da kuma gajerun rana, lokacin sanyi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Zan cika burin yan Najeriya' Matashi dan shekara 45 ya shiga tseren gaje kujerar Buhari a 2023

Watan Azumin Ramadan 2022
Ramadan 2022: Wane kasashe ne Musulmai za su kwashe awanni da yawa da awanni kaɗan a Azumin bana Hoto: islamicity.org
Asali: UGC

Shin kunsan wane ƙasashe ne a faɗin duniya da Musulmai za su fuskanci tsayin lokacin rana da kuma masu gajerun lokaci? Legit.ng Hausa ta tattaro muku su.

Dogon Azumi da Gajere a shekarar 2022

Yayin Azumin bana ƙasashen New Zealand, Paraguay, Uruguay, Argentina da kuma Afirka ta kudu ne Musulman cikinsu zasu yi gajeren Azumi da ba zai wuce awanni 11 zuwa 12.

Musulman dake zaune a birnin Reykjavík, na ƙasar Iceland, sune zasu kafa tarihi a bana na kasancewar mutanen birnin da zasu yi dogon Azumi na tsawon awanni.

Ana hasashen Musulman wannan birnin za su kame daga ci ko sha na tsawon awanni 16 da mintuna 50 yayin watan Azumin Ramadana na bana.

Sauran ƙasashen da ake tsammanin zasu yi dogon Azumi sun haɗa da Poland, Ingila, Faransa, Portugal, Greece, China, Amurka, da kuma Turkiyya.

Kara karanta wannan

An yaye tubabbun yan ta'addan Boko Haram 500 da aka yiwa horo

Ta ya Musulmi zai yi Azumi idan ƙasarsu babu dare?

Musulman dake ƙasashen da ake zuba rana tsawon lokaci ba tare da ta faɗi ba, ba zasu iya jure yin Azumi ba na tsawon awanni 20 ko fiye.

Fatawowin Malamai sun nuna cewa kasashen da tsakanin faɗuwar ranar da sake fitowarta bai wuce awa uku kacal ba, suna da damar bin tsarin yadda yan uwansu na wasu biranen ke Azumi.

Mafi yawan Musulmai a irin waɗan nan ƙasashe, alal misali sukan iya bin tsarin yadda rana ke faɗuwa da fitowa a ƙasa mai tsarki wato Saudiyya.

A watan Azumin bana, Saudiyya da mafi yawan kashen dake tsakiyar gabashin duniya za su yi azumi na tsawon awanni 15 kowace rana.

A wani labarin na daban kuma Wata Kungiya a Arewa a saya wa Atiku Abubakar Fom ɗin takarar shugaban ƙasa na PDP a 2023

Kungiyar yan kasuwan arewa maso gabas sun lale miliyoyi sun karban wa Atiku Abubakar Fom ɗin sha'awar tsayawa takara a PDP.

Kara karanta wannan

Binciken Mako: Kayan Masarufi uku da suka yi tashin gwaurin zabi a babbar kasuwar Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna tsantsar farin cikinsa tare da godiya gare su bisa wannan karamci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel