Siyasar Najeriya
Gaskiya ta bayyana kan labarin cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta bayar da umarnin cafke shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu. Bincike ya nuna ƙarya ne.
Mataimakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya gana da mambobin tsohuwar majalisar dattawa ta 9 a fadar shugaban kasa ranar Jumu'a 7 ga watan Yuli.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tura sunayen kwamishinoni 25 ga majalisar dokokin jiha, watanni Tara bayan ya karbi mulki daga hannun Oyetola a 2022.
Da Gwamnan jihar Sokoto watau Ahmad Aliyu ya shigo ofis a jiya, bai samu kowa ba sai ma’aikata 3, nan-take ya ce a rufe kofar shigowa, aka bar jami'ai a waje.
Kano- Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta yi kira tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduen ya yi watsi da gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta masa.
Babba jigo kuma tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Chief Bode George, ya gargaɗi masu hangen sauya sheka zuwa jam'iyyar APC da su canja tunani tun wuri.
Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, ya rattaba hannu kan dokar da ta zabtare yawan ma'aikatun jihar daga 28 a halin yanzu sun koma 16, ya ce haka yake so.
Majalisar dokokin Kano ta amince da naɗin mai shari'a Dije Aboki a matsayin shugabar Alkalan Kano, ta hau kujerar tun a lokacin Ganduje a matsayin rikon kwarya.
Siyasar Najeriya
Samu kari