Siyasar Najeriya
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya bayyana cewa wanda ya gada ya miƙa masa ragamar mulki babu ko naira ɗaya a asusun gwamnati, duƙ da haka ya yi aiki.
Wata gamayyar kungiyoyi CSO ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya cirewa Atiku Abubakar lambar karramawa ta GCON da ake ba mataimakan shugaban ƙasa.
Wasu jagororin addinin kirista a Najeriya sun bayyana cewa fargabar da su ke game da tikitin Musulmi da Musulmi ta gushe a yanzun bayan ganin kamun ludayin Tinubu.
Kotun ƙolin Najeriya ta kori karar da ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar SDP ya shigar kan zaben gwamnan jihar Delta wanda aka yi ranar 18 ga watan Maris. 2023.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗalibar aji 4 a jami'ar jihar Kwara a matsayin mai taimakawa kan bincike ga kwamitin sake fasalin haraji na shugaban ƙasa.
Sanatan Anambra ta kudu a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ifeanyi Ubah, ya canza sheka daga Young Progressives Party (YPP) zuwa All Progressives Congress (APC).
Kakakin LP na ƙasa, Abayomi Arabambi, ya ce Peter Obi na tattare da saɓani a takardun karatunsa musamman shaidar Digiri da kuma satifiket ɗin bautar ƙasa.
Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Ƙashim Shettima da wasu gwamnonin jam'iyyar APC 14 sun sauka a jihar Imo yayin da APC zata kaddamar da kamfe.
Gidan labarai na kasar Birtaniya, BBC, ya fitar da rahoton da ke cewa babu wata hujja dake nunaTinubu na Najeriya ya kirkiri satifiket din bogi ta Jami'ar Chicago.
Siyasar Najeriya
Samu kari