Sabon Gwamna Ya Iske Mutum 3 da Ya Mamayi Masu Zuwa Gidan Gwamnati a Makare

Sabon Gwamna Ya Iske Mutum 3 da Ya Mamayi Masu Zuwa Gidan Gwamnati a Makare

  • Mai girma Ahmed Aliyu ya tuka kan shi a mota zuwa ofishinsa da ke gidan Gwamnati a Sokoto
  • Gwamnan ya isa ofis da wuri, sai ya iske kusan duk ma’aikatan jihar ba su fito aiki tukun a lokacin ba
  • Aliyu ya umarci masu gadi su rufe makararru a waje, ya ja-kunne cewa ba zai yi wasa da amana ba

Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu ya yi abin da ya ba da mutane da-dama mamaki a ranar Alhamis, inda ya kuma yi nasarar cafke masu saba doka.

Daily Trust ta ce Ahmed Aliyu ya dauki mota, ya tuka kan shi da kan shi zuwa gidan gwamnati, a nan ya iske mafi yawan ma’aikata duk ba su iso ba.

A lokacin da Mai girma Gwamnan ya iso ofishinsa kimanin karfe 8:30 na safe ne amma ya samu jami’an gwamnati da-dama ba su ofis a lokacin.

Kara karanta wannan

‘Dan Kwankwasiyya Mai Goyon Bayan Rusau Ya Koma Salati, Rushe-Rushe Ya Zo Kan Shi

Gwamna
Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu Hoto: Hon Naseer Bazzah
Asali: Facebook

Da Gwamnan na jihar Sokoto ya shiga gidan gwamnati, bai samu kowa ba sai masu goge-goge da wata ma’aikaciyar jinya a asibitin fadar gwamnan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An bar ma'aikata a waje

Gwamna Aliyu ya bada umarni cewa masu gadi su rufe kofar shiga kuma ka da su kyale wani ma’aikaci ya shigo ciki a dalilin makarar da suka yi.

Rahoton ya nuna haka dai aka bar kofar a garkame har zuwa kusan karfe 1:00 na rana.

A cikin jerin makararrun aka bari a waje har da manyan jami’an gwamnatin jihar Sokoto da kuma hadimai da mukarraban Gwamna da aka mamaya.

Ba wasa aka fito yi ba

Da yake bayanin abin da ya jawo ya hana ma’aikatan shiga ofis, Gwamna Aliyu ya nuna bai dace a rika wasa da abin da ya shafi aikin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

A Maimakon Kujerar Minista, Shehu Sani Ya Fadi Abin da Ya Dace da Tsofaffin Gwamnoni

"Wannan ba abin wasa ba ne.
Abin da ake bukata daga duk wata gwamnati da take yi da gaske shi ne a rika biyan ma’aikata albashinsu a kan kari.
A lokacin da na zo, na biya albashin watanni biyu a cikin makonni uku.
Shiyasa na tuko kai na zuwa ofis domin direbobi a ba su da wuri ba.
Yanzu ba zan fada maku mamayar da zan yi nan gaba ba domin kuma a makare ku ka zo (yana nufin ‘yan jarida)

- Ahmad Aliyu

Jaridar ta ce Gwamnan ya nanata cewa ya yi wa al’ummar jihar Sokoto alkawari ba zai ci amanarsu ba, kuma ba zai bari wani ma’aikaci ya ci amanar ba.

Tun da ana biyan albashi a kan ka’ida, Aliyu ya ce ba za ta yiwu mutum ya ci albashi ba tare da aiki ba, idan ba haka ba zai dawo da kudin da aka biya shi.

Kara karanta wannan

Tsaro: Bukarti Ya Barranta Da Yerima, Ya Bayyana Matakin Da Ya Kamata A Dauka Akan 'Yan Bindiga

Za a binciki gwamnatin Buhari

A gwamnatin tarayya, mun ji labari za a binciki Dala miliyan 10 da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe a aikin gas a shekarar 2017.

Sanatoci sun ce Naira Biliyan 4.5 da gwamnatin tarayya ta kashe a kwangilar ya yi yawa. Barau Jibrin ya amince ayi bincike idan an kafa kwamitoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel