A Maimakon Nadin Mukami, Shehu Sani Ya Fadi Abin da Ya Dace da Tsofaffin Gwamnoni

A Maimakon Nadin Mukami, Shehu Sani Ya Fadi Abin da Ya Dace da Tsofaffin Gwamnoni

  • Sanata Shehu Sani ya bukaci Bola Ahmed Tinubu ya binciki wadanda su ka sauka daga kan mulki
  • ‘Dan siyasar ya bada shawarar a guji dawo da tsofaffin Gwamnoni da Ministoci cikin majalisar FEC
  • Yayin da ake jiran Tinubu ya kafa gwamnatinsa, tsohon Sanatan ya ce a cafke duk wada ya saci kudi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisa a 2015, Shehu Sani, ya na da ra’ayin cewa bai dace a ba tsofaffin gwamnoni mukami ba.

Tsohon Sanatan ya yi magana a dandalin Twitter, ya na nuna rashin cancantar tsofaffin Gwamnonin jihohin kasar nan su zama Ministoci.

Leadership ta rahoto Sanata Shehu Sani ya na ba Bola Tinubu shawarar ya binciki wadanda su ka rike mukamai a mulkin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Buhari a Villa, Yan Najeriya Sun Nuna Damuwa

Tinubu
Liyafar da aka shiryawa Shugaban kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Da yake tofa albarkacin bakinsa ranar Talata, ‘dan siyasar abin da ya kamata shi ne Mai girma Tinubu ya binciki wadanda suka sace dukiyar jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An damke mutane biyu

Kwamred ya yi ishara ga Godwin Emefiele da Abdulrasheed Bawa wadanda yanzu su na tsare, amma ‘yan siyasan da ake zargi da laifi su na yawo a gari.

"Ba zai zama daidai ayi tunanin sakayya ta hanyar nada tsofaffin Gwamnonin da su ka sace dukiyar jihohinsu, su ka bar jama’a a talauci da bashi ba.
Mutum biyu su na hannu a garkame, amma ba a damke sauran gungun tsofaffin masu rike madafun iko, tsofaffin Ministoci da tsofaffin gwamnonin jihohi ba.
Hakan ba zai aika sako mai kyau a lokacin da aka yi canjin gwamnati ba.

- Shehu Sani

Da wa Shehu Sani yake?

Da mutane su ke magana a shafinsa, wasu sun ce Kwamred Shehu Sani ya na nuni ne kan Nyesom Wike da ake rade-radin za a nada shi cikin Ministoci.

Kara karanta wannan

Tsaro: Bukarti Ya Barranta Da Yerima, Ya Bayyana Matakin Da Ya Kamata A Dauka Akan 'Yan Bindiga

Wasu kuma sun ce ya tabo Nasir El-Rufai ne wanda ya karbo bashin makudan kudi domin yi wa al’umma ayyuka a lokacin ya na Gwamnan jihar Kaduna.

A game da masu rike da madafan iko da tsofaffin Ministoci, a nan ma bai kama sunan kowa ba.

...Wike ya dace da mukami

A makon nan an samu rahoto cewa jigo a APC, Tony Okocha ya fadi yadda Nyesom Wike ya taimakawa Bola Tinubu/Kashim Shettima a jihar Ribas.

Tun 1999, PDP ta saba samun nasara a jihar Kudu maso kudancin kasar, Okocha ya ce sai a zaben 2023 Wike ya takawa takarar Atiku Abubakar burki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel