‘Dan Kwankwasiyya Mai Goyon Bayan Rusau Ya Koma Salati, Rushe-Rushe Ya Zo Kan Shi

‘Dan Kwankwasiyya Mai Goyon Bayan Rusau Ya Koma Salati, Rushe-Rushe Ya Zo Kan Shi

  • Muhammad Suleiman Musa ya na cikin wadanda Gwamnatin Kano za ta rusa masu shaguna a kasuwa
  • ‘Dan kasuwan ya na cikin mabiya darikar Kwankwasiyya, ya na cikin wadanda ke tare da Abba Gida Gida
  • Ganin ruguza gine-ginen da ake yi ya zo kansa, hakan ya nemi ya taba imanin Muhammad Suleiman Musa

Kano - Wani ‘dan kasuwa mai suna Muhammad Suleiman Musa ya zama abin magana a dandalin sada zumunta a dalilin shirin rusa shagonsa.

Daga kalamansa a shafin Facebook, za a fahimci Malam Muhammad Suleiman Musa ya na cikin masu goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya a Najeriya.

Har ta kai ‘dan kasuwan ya na fitowa fili wajen nuna goyon bayansa ga rushe-rushen wasu wurare da Gwamnatin Abba Kabir Yusuf take yi a fadin jihar.

Kwankwasiyya
Wani 'Dan Kwanwasiyya Hoto: Aminu88, www.heavyequipmentrentals.com
Asali: UGC

Abba ka rusa, ka gyara Kano

Kara karanta wannan

Hukumar NEMA Ta Kawo Jerin Jihohi 14 Da Za a Fuskanci Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan

Da ake lalubo maganganun da ya yi a baya, wannan matashi ya taba kira ga sabon Gwamnan Kano ya ruguza jihar idan ta kama domin ayi gyara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwatsam sai aka ji shi a shafin Facebook ya na rangada salati bayan jami’an gwamnati sun yi wa shagonsu a kasuwa fenti da nufin ruguza shi.

Ganin ana kokarin rusawurin neman abincinsa, Muhammad Suleiman Musa ya yi kira ga Gwamna Abba da ya rika sara yana duba bakin gatarinta.

A cewarsa ba su dade da kama hayar shagon ba, sai ga shi an yi masa jen fenti, ‘dan kasuwan ya ke kukan cewa shagon ne hanyar neman abincinsu ba.

Innalillahi wa inna Ilahi rajiun !!

"Allahumma ajirni filmusibati waaklifni kairanminha!
ABBA ka na sara ka na duba bakin gatarinka kaso 80 cikin 100 na shagunanan da kake rushewa na masoyan ka ne.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso Ya Musanta Zargin Juya Abba Gida Gida, Ya Ce Talaka Aiki Yake Bukata Ya Gani A Kasa

Wata biyu kenan da kama wannan shagon namu, amma yau ka sa mana Jan fenti. Wannan shine sakamakon gwagwarmayar da mu kayi a kan ka?
Lallai ka na saka mana da abinda ya dace idan mu ka daina zuwa kasuwar me za muyi? Allah ka iyamana da iyawarka."

- Muhammad Suleiman Musa

Ko yanzu a koma filin zabe

Daga baya kuma an ji shi ya na bayani a shafin na sa, a nan ya nuna duk abin da zai faru bai yi nadamar zaben Abba Kabir Yusuf a takarar Gwamna ba.

Ko yau za a koma filin zabe, Muhammad Musa ya ce jam’iyyar NNPP zai dangwalawa kuri’arsa.

"Don haka ba na kalubalantar wannan gwamnatin domin ta taba mani shago. Har gobe muna fada duk inda aka yi kuskure, ABBA ka rushe.
Masu dariya ba za ka hana su ba, bakin su ne amma mu ‘yan gwagwarmaya ne na kwankwasiyya har gobe sai fatan nasara a rayuwa, tarbiyar siyasar mu har gobe mu na alfahari da ita."

Kara karanta wannan

“Buhari Yana Landan Don Jinya Kamar Yadda Ya Saba”, Rafsanjani Ya Yi Zargi

- Muhammad Suleiman Musa

An yi nadin mukamai a Kano

A yau aka ji labari Ahmadu Danzago ya zama shugaban hukumar da ke tattara shara a Kano, Sanusi Kwankwaso ya zama mai ba Gwamnan jihar shawara.

Sanarwar ta ce wadanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada za su fara aiki ba tare da bata lokaci ba, a cikinsu akwai Ambasada Yusuf Imam Ogan Boye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel