Shugaba Tinubu Na Gana Wa da Shugaban APC Na Kasa da Sakatare a Villa

Shugaba Tinubu Na Gana Wa da Shugaban APC Na Kasa da Sakatare a Villa

  • Shugaba Tinubu ya shiga ganawar sirri yanzu haka da shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da sakatare, Iyiola Omisore a Aso Rock
  • Wannan taro na zuwa ne awanni 24 bayan Adamu ya ce APC ba ta da hannu a sabbin jagororin majalisa ta 10 da aka sanar
  • Lamarin dai ya bar baya da ƙura a jam'iyyar APC mai mulki kuma ana hasahen shi ne dalilin wannan zama a Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na ganawa yanzu haka da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, da sakataren jam'iya, Iyiola Omisore a Aso Rock, Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jiga-jigan biyu sun dira fadar shugaban ƙasa mintuna kalilan kafin ƙarfe 5:00 na yamma ta cika ranar Laraba, 5 ga watan Yuli.

Shugaba Tinubu na ganawa da Adamu da Sakataren APC.
Shugaba Tinubu Na Gana Wa da Shugaban APC Na Kasa da Sakatare a Villa Hoto: punchng
Asali: UGC

Daga isarsu, suka wuce kai tsaye zuwa ofishin shugaban kasa suka fara taron a sirrance, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon Rahoto Ya Bayyana Sunayen Manyan Yan Siyasa Da Wasu Da Ka Iya Shiga Jerin Ministocin Tinubu

Wannan gana wa na zuwa awanni 24 bayan APC ta nesanta kanta da sunayen jagororin majalisar tarayya da aka sanar ranar Talata, 4 ga watan Yuli 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu saɓani a jam'iyyar APC kan kujerun jagororin majalisa ta 10

Idan baku manta ba APC ta ce bata da alaƙa da sabbin jagororin majalisa da aka ji shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, sun sanar a zauren majalisa.

Yayin taro da gwamnonin jam'iyyar APC ƙarƙashin jagorancin gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, Sanata Abdullahi Adamu ya ce:

"Yanzu nake ganin jita-jita a kafafen sada zumunta na zamani cewa an yi wasu sanarwa a majalisar dattawa da majalisar wakilan tarayya."
"Hedkwatar jam'iyyar APC ta ƙasa, kwamitin gudanarwa (NWC) bai tura wani sako ko isar da saƙo ga majalisa game da zaɓen jagoraorin majalisa ta 10 ba."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP 2 a Aso Villa

"Kuma daga nan zuwa lokacin da zamu cimma matsaya mu tura musu kamar yadda aka saba, duk abinda shugaban majalisar dattawa, mataimakinsa, kakaki ko mataimaki suka sanar ba daga mu bane."

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jiga-Jigan PDP a Aso Villa

A wani labarin na daban kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin tsohon shugaban majalisar dattawa, Chief Pius Anyim da Olisa Metuh a Villa.

Mista Anyim da Metuh, waɗanda duk sun riƙe mukamin Sakataren watsa labaran PDP na ƙasa, sun isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 1:30 na rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel