Siyasar Najeriya
Shugabannin kananan hukumomin jihar Kano 44 sun nuna sam ba su yarda da yunkurin gwamnatin jihar Kano na talauta asusun baitul mali wajen gida gadoji ba.
Gwamnatin jihar Ekiti ta ayyana zamam makokin kwanaki 3 da sauke tutoci zuwa ɗabi domin nuna alhini da girmama marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo na ci gaba da laluben mutum mai tsantaar biyayya wanda zai masa mataimakin gwamna bayan rantsar da shi ranar Laraba.
Razaq Aderibigbe, jigon NNPP mai kayan marmari ya bayyana yaƙini cewa kotun kolin Najeriya zata tabbatar da adalci a shari'ar zaben gwamnan Kano da ke gabanta.
Primate Ayodele ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara zai ka.jam'iyyar APC nan gaba kaɗan domim ba zai iya jure faɗansa da ministan Abuja, Nyesom Wike ba.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya zama mutum na farko da ya fara biyan albashin wata 13 a shekara ɗaya ga ma'aikatan gwamnati a tarihin jihar.
Mutanen da tsohon gwamnan jihar Ondo, Marigayi Rotimi Akeredolu, ya naɗa a muƙamai na ci gaɓa da miƙa takardar murabus bayan rasuwarsa ranar Laraba.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta jaddada cewa ba gudu ba ja da baya dukkan yan majalisar jihar Ribas da suka sauya sheƙa zuwa APC sun rasa kujerunsu.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tara masu buƙata ta musamman akalla 2,000 a gidan gwamnati, ya raba musu tallafin N20,000 kowanen su da kayan abinci.
Siyasar Najeriya
Samu kari