Ondo: Tinubu Ya Shiga Tsakani Yayin da Fafutukar Zama Mataimakin Gwamna Aiyedatiwa Ya Fara

Ondo: Tinubu Ya Shiga Tsakani Yayin da Fafutukar Zama Mataimakin Gwamna Aiyedatiwa Ya Fara

  • Akwai alamu da ke nuna cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana matukar kishin siyasar jihar Ondo
  • An rahoto cewa shugaba Tinubu ya sa baki wajen neman sabon mataimakin gwamnan jihar
  • Yayin da ba a bayyana wanda shugaban kasar ya fi so a hukumance ba, an ambaci wasu sunaye a matsayin wadanda ke kan gaba wajen neman takarar kujerar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Akure, Jihar Ondo - Kimanin kwanaki biyu bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa na fuskantar sabon kalubale dangane da zabar mataimakinsa yayin da yake shirin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Rahotanni sun nuna cewa Aiyedatiwa, wanda ya hau kan karagar mulki bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, na fuskantar matsin lamba don ya bayyana mataimakinsa, wanda zai taimaka masa wajen gudanar da mulkin jihar.

Kara karanta wannan

"Ya hadu": Wani mai zanen gida ya kafa tarihi, ya gina zagayayyen gida a kauyensa

Tinubu ya nuna sha'awarsa a siyasar Ondo
Ondo: Tinubu Ya Shiga Tsakani Yayin da Fafutukar Zama Mataimakin Gwamna Aiyedatiwa Ya Fara Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Majiyoyi na nuni da cewa zabar mataimaki na iya zama kalubale ga Aiyedatiwa, duba da rudanin siyasa da rashin jituwar da ke tattare da zamansa gwamna bayan rasuwar Akeredolu.

Ana rade-radin cewa Aiyedatiwa na iya dauko mataimakinsa daga majalisar da ke kasa, musamman wadanda suka mara masa baya a lokacin rikicin siyasa da ya yi barazana ga wa'adin mulkinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan na duba bangarori daban-daban, inda yake duba yiwuwar zabar mataimaki daga mazabar Ondo ta tsakiya ko kuma yankin Ondo ta Arewa, wanda ya yi daidai da shiyyar marigayi Akeredolu.

Gwamnan Ondo ya fara tuntuba kan wanda zai ama mataimakinsa, yayin da sunayen suka bayyana

Babban abun, an bayyana cewa Aiyedatiwa, ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da kungiyoyi a ciki da wajen jihar, don yin taka tsan-tsan wajen zabo mataimakinsa, inda yake la'akari da burinsa na son tsayawa takarar gwamna a 2024.

Kara karanta wannan

Ta fasu: Jerin sunayen 'yan siyasa 2 da ɗayansu ka iya zama sabon mataimakin gwamnan APC

Aiyedatiwa, wanda dan asalin Ilaje ne a gundumar Ondo ta Kudu, yana da niyan neman kujerar gwamnan na Alagbaka har sai da dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da marigayi gwamnan.

Rikicin siyasa ya barke tsakaninsa da ubangidan nasa, wanda ya kai ga an far shirin tsige Aiyedatiwa bisa zargin rashin biyayya.

Majalisar dokokin jihar karkashin Kakakin Majalisar, Olamide Oladiji, ta tuhume shi kan abubuwa 14 da suka hada da keta haddin kujerarsa, facaka da kudi, da yin wallafa da ke bata sunan gwamnan.

Majiyoyi sun nuna cewa masu neman kujerar mataimakin gwamna a majalisar zartarwar jihar sun hada da Mista Rasaq Obe, kwamishinan makamashi da albarkatun ruwa da kuma Mista Olugbenga Ale, shugaban ma’aikatan marigayi Gwamna Akeredolu.

Obe, daga Ilara Mokin, ya nuna biyayya ga Aiyedatiwa ta hanyar fallasa labaran karya a cikin majalisar zartarwa, yayin da Ale, daga Owo, ya fuskanci zarge-zargen rashin biyayya bayan ya kamu da rashin lafiya tare da jinkirta mika mulki.

Kara karanta wannan

2024: Kwanaki 2 da mutuwar gwamna, Lucky ya manta da shi ya ziyarci Tinubu kan wani babban dalili

Masu goyon bayan Ale sun bayyana cewa nadinsa zai daidaita al’amuran siyasa a jihar, inda zai zama diyya ga Akeredolu, wanda ya kasa kammala wa’adinsa kafin rai ya yi halinsa.

Shugaba Tinubu ya shiga tsakani

Sai dai kuma, yayin da ake fafutukar kujerar mataimakin gwamna, wata majiya a cikin gwamnatin ta sanar da jaridar Daily Trust cewa Shugaban kasa Bola Tinubu, wanda ya shiga harkokin siyasar jihar, ya rigada ya sa baki wajen zabar mataimakin Aiyedatiwa.

Majiyar ta bayyana cewa Tinubu ya yi amfani da karfinsa ne a ranar Alhamis inda ya gayyaci Aiyedatiwa zuwa wata ganawar sirri a gidan shugaban kasa na Ikoyi da ke Lagas.

A yayin wannan taro an tattauna sosai kan batun kujerar mataimakin gwamnan.

Duk da rashin amincewa da wasu abubuwan da Aiyedatiwa ya yi bayan rasuwar Akeredolu, shugaban kasar ya jaddada cewa bai kamata zaben mataimakin ya zama wani sabon rikicin siyasa a jihar ba.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: Jerin hadiman gwamna da suka yi murabus daga muƙamansu bayan mutuwa ta gitta

Wanene dan takarar APC?

Yayin da ake ci gaba da hasashen kan zabar mataimakin Aiyedatiwa, bincike ya nuna cewa shugabancin jam'iyyar APC na duba yiwuwar daura Ifedayo Abegunde kan wannan mukami.

Abegunde, wanda aka fi sani da Abena, shi ke rike da mukamin babban daraktan kula da harkokin kamfanoni a hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) a yanzu haka, nadin da shugaban kasa ya yi kwanan nan.

Abegunde wanda ya fito daga yankin Akure, ya rike da mukamin sakataren gwamnatin jihar (SSG) a lokacin wa’adin mulkin Akeredolu na farko, amma ya raba gari da tsohon gwamnan bayan zaben fidda gwani, wanda ya kai ga cire shi daga mukaminsa a wa’adi na gaba.

Majiya mai tushe daga cikin jam’iyyar ya yi nuni ga cewar fadar shugaban kasar na kokari, tare da goyon bayan shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Ganduje wajen ganin an zabo Abegunde a matsayin mataimakin gwamna.

Kara karanta wannan

Awanni kadan bayan shiga ofis, sabon Gwamna Lucky ya nada mukamai, ya yi wani gagarumin abu 1

Sunayen masu neman mataimakin gwamnan Ondo

A wani labarin, mun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya fara lalube da binciken wanda zai ɗauko a matsayin mataimakin gwamna.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito ranar Jumu'a, 27 ga watan Disamba, Gwamna Aiyedatiwa ya fara faɗi tashin neman wanda zai taya shi shugabanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel