Gwamnan APC Ya Ayyana Zaman Makokin Kwanaki Uku a Jiharsa Kan Babban Rashin da Aka Yi

Gwamnan APC Ya Ayyana Zaman Makokin Kwanaki Uku a Jiharsa Kan Babban Rashin da Aka Yi

  • Gwamna Oyebanji na jihar Ekiti ya ayyana zaman makokin kwanaki uku domin jimamin rasuwar shugaban gwamnonin kudu
  • Biodun Oyebanji ya kuma bada umarnin sauke dukkan tutocin gwamnati zuwa rabi domin girmama marigayi Akeredolu
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Gwamna Akeredolu na jihar Ondo ya riga mu gidan gaskiya a ƙasar Jamus

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji, ya ayyana hutun kwanaki uku na zaman makokin Gwamna Arakunrin Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Akeredolu ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin kudu da gwamnonin kudu maso yamma har zuwa lokacin da Allah ya masa rasuwa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti.
Gwamnan APC Ya Ayyana Zaman Makokin Kwanaki Uku a Jiharsa Kan Babban Rashin da Aka Yi Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Ondon ya rasu ne ranar Laraba, 27 ga watan Disamba. 2023 bayan fama da doguwar jinya a asibitin ƙasar Jamus.

Kara karanta wannan

Ta fasu: Jerin sunayen 'yan siyasa 2 da ɗayansu ka iya zama sabon mataimakin gwamnan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Ekiti ta fara zaman makoki

Gwamna Oyebanji ya bi sahun takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde ya ayyana zaman makokin kwanaki uku a jihar Ekiti domin jimamin rasuwar Akeredolu.

Wannan mataki da gwamnan na APC ya ɗauka na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Yinka Oyebode, ya fitar da safiyar ranar Jumu'a, 29 ga watan Disamba.

Rahoton Tribune ya ce dukkan tutoci a gine-ginen gwamnati da ke fadin jihar za a sauke su zuwa rabi na tsawon kwanaki uku da za a shafe ana zaman makoki in ji sanarwan.

Tun da fari dai Gwamna Oyebanji miƙa sakon ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar jihar Ondo bisa rasuwar marigayi Gwamna Akeredolu.

Amma duk da haka, Gwamnan ya kai ziyarar ta'aziyyar wannan babban rashi ga iyalan marigayin a gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kara karanta wannan

2024: Kwanaki 2 da mutuwar gwamna, Lucky ya manta da shi ya ziyarci Tinubu kan wani babban dalili

Idan dai baku manta ba a baya gwamnan jihar Oyo, Mista Seyi Makinde, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a jihar sa domin girmama marigayi Akeredolu.

Wa zai zama sabon mataimakin gwamna a Ondo?

A wani rahoton na daban An sake shiga ruɗani da rashin tabbas kan naɗa sabon mataimakin gwamna a jihar Ondo amma dai gwamna na ta laluben wanda ya dace.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Lucky Aiyedatiwa ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Ondo ranar Laraba, 27 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel