Gwamna Abba Ya Sake Bada Mamaki a Kano Yayin da Kotun Koli Ke Dab da Yanke Hukunci

Gwamna Abba Ya Sake Bada Mamaki a Kano Yayin da Kotun Koli Ke Dab da Yanke Hukunci

  • Gwamna Abba Gida-Gida ya raba N20,000 ga mutane masu buƙata ta musamman (PWD) 2000 kowanen su a jihar Kano
  • Da yake jawabi a wurin rabon tallafin, Gwamnan ya ce wannan somin taɓi ne domin ya san gudummawar da suka ba shi har ya ci zaɓe
  • Ya kuma bada umarnin a ƙara musu da buhunan kayan abinci domin sauƙaƙa musu halin da ake ciki na wahalar rayuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rabawa mutane masu buƙata ta musamman tallafin N20,000 a sassan jihar, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Gwamnan ya rabawa masu buƙata ta musamman watau nakasassu 2000 tallafin kuɗin ne a wani yunƙuri na ganin sun dogara da kansu.

Kara karanta wannan

Apapa: Sabon rikici ya ɓalle a jam'iyyar adawa yayin da aka lakaɗa wa wasu jiga-jigai 2 dukan kawo wuƙa

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Kano: Gwamna Yusuf Ya Rabawa Nakasassu 2,000 Tallafin N20,000 Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Da yake jawabi a wurin kaddamar da bada tallafin wanda ya gudana a Coronation Hall ranar Alhamis, Gwamna Abba ya ce tallafin na ɗaya daga cikin alkawurran da ya yi lokacin kamfe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana shirin raba tallafin a matsayin wani yunƙuri na karfafa musu guiwa yayin da gwamnatinsa ke kokarin agaza wa naƙasassu da iyalansu a Kano.

Abba ya ƙara da cewa ya ji daɗin yadda ya shiga zuƙatan masu buƙata ta musamman, yana mai jaddada cewa da goyon bayansu ya samu nasara a zaben 18 ga watan Maris.

Dalilin rabawa naƙasassu tallafi - Abba

Ya ce wannan tallafin da aka raba wa nakasassun kamar wani lada ne bisa ɗumbim goyon bayan da suka baiwa gwamnatinsa, kuma a cewarsa somin taɓi ne.

Abba Kabir ya ce:

"Mun gayyato ku nan gidan gwamnati ku karɓi tallafin ne saboda mu ƙara tabbatar da cewa gwamnatin mu tana mu'amala da kowa ba tare da duba halittar su ta zahiri ko kuɗinsu ba."

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya damƙa ƙananan yara 7 hannun Iyayensu bayan ceto su, ya tura saƙo ga gwamnan Bauchi

“Baya ga tallafin tsabar kudi, na ba da umarnin a raba muku buhunan kayan abinci. Ya kamata a baku kayan abinci ko da kuwa kun samu a baya."
"Kuna da mahimmanci a gare mu, kuma za mu yi duk abin da zai yiwu don tallafa muku. Muna sane da gagarumin goyon bayan da kuke ba gwamnatinmu, wanda shi ne mabudin nasarar zabenmu."

Wani mamban NNPP a Kano, Abdullahi Sa'idu, ya nuna jin daɗinsa da tallafin, inda ya shaida wa Legit Hausa cewa ɗan uwansa na cikin waɗanda suka amfana.

Ya ce:

"Tabbas ina da labari, domin akwai wani ɗan uwana mai nakasa yana cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin. Na ji ana cewa sai kana da hanya, gaskiya ba haka bane."

A cewarsa, gwamnatin NNPP ta kowa ce matuƙar kai ɗan Kano ne, "ko ka zaɓe mu ko baka zaɓe mu ba, zamu yi kokarin yi ma kowa adalci."

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka bai wa ma'aikatan jihohinsu kyautar N100,000 a ƙarshen 2023

Gwamna Makinde ya ayyana hutun makoki

A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Oyo ya ayyana hutun kwana uku na zaman makokin rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Makinde, mataimakin shugaban gwamnonin Najeriya tare da gwamnan Kwara sun ziyarci gidan marigayin na Ibadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel