Siyasar Najeriya
Bayan lalacewar babban layin wutar lantarki na ƙasa sau 3 a mako guda, matasa sun fara kiran a tsige ministan makamashi, Adebayo Adelabu da shugaban TCN.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake dage taron majalisar zartaswa na kasa (NEC) wanda ta shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Oktoban 2024.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP ta kara faɗawa cikim rigima yayin da tsagin Gwamna Bala Mohammed ya maka ƙara a gaban kotun kan taron NEC.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta haramta gudanar da zaben ciyamomi da kansilolin da aka shirya yi a Kano ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba.
Rikicin PDP kan zaben 2027 a kara ƙamari yayin da ake ƙoƙarin juya baya ga Atiku Abubakar. Yan bangaren Nyesom Wike sun fara goyon bayan gwamnan Oyo a kan Atiku.
Tsohon mataimaƙin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya taya jagoran NNPP murnar cika shekara 68 a duniya, ya ce Kwankwaso mutum ne da ya yiwa Najeriya aiki.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya ce jami'o'in da ya gima lokacin mulkinsa sun fi faranta masa rai fiye da gadoji da titunan da ya gina.
Prince Adewole Adebayo ya ce ba zai dhiga duk wata ƙawancen siyasa ba matuƙar zuciya ba ta zo ɗaya ba, ya ce Buhari da Tinubu kadai sun isa misali.
Abba Kabir Yusuf ya taya Rabi'u Kwankwaso murnar ranar haihuwa. Kwankwaso ya cika shekaru 68 da haihuwa a duniya. Abba ya shafe shekaru 38 tare da Rabi'u Kwankwaso.
Siyasar Najeriya
Samu kari