An Kunyata Tinubu Wajen Rantsar da Shugaban Afrika ta Kudu? An Fayyace Gaskiyar Lamarin

An Kunyata Tinubu Wajen Rantsar da Shugaban Afrika ta Kudu? An Fayyace Gaskiyar Lamarin

  • Fadar shugaban kasar Najeriya ta ƙaryata bidiyon da ake yadawa kan kunyata Bola Tinubu a kasar Afrika ta Kudu
  • An yi yada wani faifan bidiyo da ke nuna Cyril Ramaphosa ya ki gaisawa da Shugaba Bola Tinubu yayin taron rantsar da shi.
  • Daga bisani, fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu ta wallafa bidiyon Ramaphosa da Tinubu suna gaisawa cikin mutuntawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

South Africa - Fadar shugaban kasa ta ƙaryata labarin da ake yadawa cewa an kunyata Bola Tinubu a kasar Afrika ta Kudu.

An yi ta yaɗa labarin cewa shugaban kasar, Cyril Ramaphosa ya ki gaisawa da Mai girma Bola Tinubu yayin bikin rantsar da shi.

Kara karanta wannan

Sarkin da ya fi daɗewa a sarauta a Arewa ya rasu, Bola Tinubu ya tura saƙon ta'aziyya

Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan bidiyon da ake yadawa na Tinubu a South Africa
Gwamnatin Tarayya ta fayyace gaskiya kan faifan bidiyon Tinubu a South Africa da ake yadawa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Bidiyon Tinubu ya ta da kura

Yar gwagwarmyar nan, Aisha Yesufu ta wallafa wani faifan bidiyo a shafin X inda ta ce an kunyata Tinubu yayin da Ramaphosa yaki gaisawa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon Ramaphosa na gaisawa da Tinubu

Sai dai daga bisani, fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu ta wallafa wani faifan bidiyo inda aka gano suna gaisawa da Tinubu.

"Mai girma shugaban kasa, na ji dadin ganinka a nan, za mu yi magana daga baya, ina matukar godiya."

- Ramaphosa ga Tinubu

Bola Tinubu ya yi martani kan lamarin

Har ila yau, hadimin Tinubu a bangaren yada labarai, O’tega Ogra ya ce mai gidansa na layi na biyu inda aka ware sahun farko saboda masu sarauta na Afrika ta Kudu.

Ogra ya ce Ramaphosa ya fara gaisawa da wadanda ke gaba, sai aka kira shi ya zauna saboda lokacin gaisuwar bai yi ba.

Kara karanta wannan

"Ba a nan kawai ake wahala ba," Shugaba Tinubu ya gargadi jama'an Najeriya

Ya ce daga bisani Ramaphosa ya zagaya har inda su Tinubu ke zaune a sahu na biyu inda suka gaisa cikin mutunta juna.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani shugaban kungiyar matasa ta NYPI, kan cece-kuce da ake game da bila Tinubu.

Kwamred Salihu Musa ya ce wannan rashin kishin kasa ne ma ace mutum yana tada jita-jita kan irin wannan lamari.

Kowa ya sani babu wani abu makamancin haka da ya faru saboda shugaban Afirka ta Kudu ya wallafa bidiyon da suke gaisawa da Tinubu.

Ya shawarci matasa da su zama masu kishin kasa domin inganta Najeriya baki daya.

Shugaba Tinubu ya tafi South Africa taro

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa birnin Pretoria na ƙasar Afrika ta Kudu.

Shugaban ƙasan ya bar birnin Lagos ne da misalin ƙarfe 11:06 na safe a ranar Talata, 18 ga watan Yuni domin zuwa ƙasar ta Afrika ta Kudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.