PDP Ta Garzaya Kotu Kan Batun Tsige Shugabanta Na Kasa, Ta Nemi Wata Bukata

PDP Ta Garzaya Kotu Kan Batun Tsige Shugabanta Na Kasa, Ta Nemi Wata Bukata

  • Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta ƙalubalanci umarnin da kotun tarayya ta ba da na hana ta sauke shugabanta na ƙasa, Umar Damagum
  • Jam'iyyar ta buƙaci kotun da ta yi watsi da shari'ar gaba ɗayanta wacce ke neman a tsige shugaban na riƙo daga kan muƙaminsa
  • Mai ba PDP shawara kan harkokin shari'a ya ce sun shigar da ƙorafin ne saboda batun tsige Damagum lamari ne na cikin gida a jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta ƙalubalanci umarnin babban kotun tarayya na hana ta sauke shugabanta na ƙasa, Umar Damagum.

Umar Damagum wanda ya taɓa zama mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa (Arewa) ya zama shugaban riƙo na kasa bayan da kotu ta dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Kano: NNPP tayi martani, ta ce APC na yunƙurin ƙwace mulki daga Gwamna Abba

PDP ta kalubalanci hukuncin kotu kan Umar Damagum
PDP ta bukaci kotu ta yi fatali da karar neman tsige Umar Damagum Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

A kwanakin baya ne dai babbar kotun tarayya ta hana PDP tsige Damagum ko maye gurbinsa har sai ta yi hukunci kan ƙarar da ke gabanta mai lamba FHC/ABJ/CS/579/2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa jam'iyyar PDP ta shigar da ƙorafin?

A wata tattaunawa da jaridar Punch, mai bai jam’iyyar PDP shawara kan harkokin shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN), ya bayyana cewa jam’iyyar ta shigar da ƙorafin.

Ajibade ya ce jam’iyyar na buƙatar kotu ta yi watsi da shari'ar, inda ya ce lamarin cikin gida ne.

Ya ƙara da cewa a ranar 1 ga watan Yuli ne kotun za ta saurari ƙarar.

"Ba mu buƙatar ɗaukaka ƙara saboda ba a yanke hukunci ba. Abin da suka samu shi ne hukuncin wucin gadi, amma za a saurari ƙarar domin duba cancantar ta a ranar 1 ga watan Yuli."
"Jam’iyyar ta shigar da ƙorafinta. Babban abin da ke a cikin ƙorafin jam’iyyar shi ne, muna roƙon kotu da ta yi watsi da shari’ar domin al’amarin cikin gida ne na jam’iyyar."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya dau zafi yayin da aka kori tsohon dan majalisa ana dab da zaben gwamna

- Kamaldeen Ajibade SAN

PDP ta kori Philip Shaibu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta kori tsohon mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamred Philip Shaibu daga cikinta.

Jam'iyyar ta ɗauki matakin ne bayan ta zargi Philip Shaibu da cin dunduniyarta ana saura watanni uku a gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng