Jam'iyyar PRP Ta Bayyana Kuskuren Tinubu da Ya Jefa 'Yan Najeriya Cikin Wuya

Jam'iyyar PRP Ta Bayyana Kuskuren Tinubu da Ya Jefa 'Yan Najeriya Cikin Wuya

  • Jam'iyyar adawa ta PRP ta caccaki manufofin tattalin arziƙin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsiro da su ƙasar nan
  • PRP ta ce ko kaɗan manufofin ba su dace ba domin babu abin da suka jawo sai wahala da shiga cikin halin ƙunci ga ƴan Najeriya
  • Ta yi kira ga gwamnatin da ta gaggauta sauya manufofin tare da mayar da hankali wajen yin abubuwan da su amfani ƴan ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PRP ta soki manufofin tattalin arziƙi da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke aiwatarwa a ƙasar nan.

Jam'iyyar PRP ta bayyana manufofin a matsayin masu cutarwa ga al’ummar Najeriya.

PRP ta caccaki gwamnatin Tinubu
Jam'iyyar PRP ta soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Jam'iyyar PRP ta soki gwamnatin Bola Tinubu

Kara karanta wannan

"Ba ku kadai ba ne": Tinubu ya magantu kan talauci a kasa, ya kawo mafita

Jam'iyyar ta nuna takaicinta kan abin da ta bayyana yadda gwamnatin ba ta damu da halin ƙuncin da manufofinta suka jawowa ƴan Najeriya ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam'iyyar PRP na ƙasa, Dr. Falalu Bello, a cikin wata sanarwa ya ce wannan gwamnatin ba ta damu da wuyar da talaka ke sha ba, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

PRP ta fadi kuskuren Tinubu a mulki

Ya nuna cewa gwamnatin ta dogara kan wasu manufofin tattalin arziƙi na ƙasashen waje waɗanda tarihi ya nuna cewa ba su taɓa yin nasara ba.

PRP ta buga misalai da wasu manufofin da bankin duniya da hukumar IMF suka amince da su a shekarun baya, waɗanda suka jawo koma bayan tattalin arziƙi a ƙasashen Afirika da Amurka.

Jam'iyyar da ta fi kowace daɗewa a ƙasar nan ta ce yawan ƙarin haraji da kuɗin ruwan da ake yi ya saɓawa hankali, musamman duba da yadda wuraren kasuwan ciki har da manya kamfanonin ƙasashen waje ke kullewa.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya nemi muhimmiyar bukata wajen 'yan Najeriya kan Bola Tinubu

Ta kuma koka kan yadda masu kamfanoni ke shan wahala sakamakon cire tallafin man fetur, karya darajar Naira, ƙarin kuɗin lantarki da hauhawar farashin kayayyaki.

Wace mafita jam'iyyar PRP ta kawo?

PRP ta yi nuni da cewa akwai hanyoyin tattalin arziƙi da za a bi waɗanda za su samar da abubuwan da ake buƙata ba kamar na yanzu ba da suka jawo wahala.

Ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta sauya waɗannan manufofin nata, sannan ta buƙace ta da ta ba da fifiko wajen jin daɗin ƴan ƙasar.

Tinubu ya ba ƴan Najeriya haƙuri

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya lallabi ƴan Najeriya da cewa ba a kasar nan kadai ake shan wahala da matsin da ake ta ƙorafi a kai ba.

Tinubu ya bayyana cewa matsalar ta shafi ko'ina a duniya amma zai iya bakin ƙoƙarinsa domin kawo gyara ta yadda ƴan Najeriya za su samu sauƙi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng