PDP ta Tsoma Baki kan Rikicin Ribas, Yayin da APC ke Neman a Sanya Dokar ta Baci

PDP ta Tsoma Baki kan Rikicin Ribas, Yayin da APC ke Neman a Sanya Dokar ta Baci

  • Jam’iyyar PDP ta tofa albarkacinta kan yadda ake ci gaba da rikicin siyasa a jihar Ribas inda ta roki tsofaffin shugabannin kananan hukumomin jihar da su guji tayar da zaune tsaye
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi wanda wa’adinsu ya cika a makon da mu ke ciki
  • Jam’iyyar ta cikin sanarwar da sakataren yada labaranta, Mista Debo Ologunagba ya bayyana cewa kamata ya yi dukkanin al’umar jihar su tabbata sun taimaka wajen zaman lafiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Rivers- Jam’iyyar PDP ta tsoma baki cikin rikicin siyasa da ke daukar sabon salo a jihar Ribas, inda ta gargadi shugabannin kananan hukumomi da wa’adinsu ya zo karshe su guji tayar da tarzoma.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Mista Debo Ologunagba ne ya bayar da shawarar a sanarwar da ya fitar ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja.

Fubara
PDP ta nemi tsofaffin kananan hukumomi su guji tayar da rigima Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

A wani labarin da Vanguard News ta wallafa, Ologunagba ya kara da cewa tabbas wa’adin shugabancin kananan hukumomi na shekaru uku ya zo karshe kamar yadda doka ta tanada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A bi doka,” PDP ga jama’an Ribas

Jam’iyyar PDP ta nemi al’ummar jihar Ribas da ka da su dauki zafi yayin da rikicin siyasar jihar ke kara kamari bayan gwamnati ta tabbatar da zuwan wa’adin shugabannin kananan hukumomi ya zo karshe.

Nigerian Tribune ta ce jam’iyyar ta bayar da shawarar ne a yau, inda ta kuma shaida kara wa’adin sayar da takardar neman tsayawa takara a yayin babban taron da da zai gudana a 2024.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a Ado Bayero Mall a Kano, har yanzu ana kokarin kashe wutar

Tun da farko jam’iyyar ta sanya 17 Yuni 2024 da cewa ita ce ranar da za a rufe sayar da takardar, amma yanzu an kara wa’adin zuwa Juma’a Yuni 28, 2024.

An rantsar da ciyamomi 23 a Ribas

A baya mun kawo labarin cewa gwamnatin jihar Ribas ta yi watsi da rigingimun siyasar jihar sannan ta rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar bayan wa’adin tsofaffin ya zo karshe.

Gwamna Siminalayi Fubara ne ya rantsar da shugabannin a fadar gidan gwamnati da ke babban birnin jihar a Fatakwal cikin tsauraran matakan tsaro domin gudun rikici.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.