Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Sarki Aminu Ado Bayero ba ya a cikin Kano yanzu haka a yayin da Sarkin Kano na 14, Alhaji Muhammadu Sanusi II ke kan hanyarsa ta komawa kan karagar mulki.
A yau Alhamis 23 ga watan Mayu, majalisar dokokin jihar Kano ta amince da rusa duka masarautun jihar guda biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.
Ashraf Sanusi, dan tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya ce majalisar dokokin jihar Kano ta gyara zalincin da aka yi wa mahaifinsa a shekaru biyar da suka wuce.
Shugaban masu rinjaye a majalisar Kano, Lawan Hussaini Dala ya ce majalisar jihar ta soke masarautu 5 na jihar domin dawo da daraja da al’adar jihar Kano.
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da rusa dukkan masarautun biyar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro lokacin da yake gwamna.
Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa an mayar da Sanusi Lamido Sanusi kan kujerar Sarkin Kano bayan majalisar jihar ta rushe sarakuna 4 da aka kara.
Mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar dokokin jihar Kano sun fice daga zauren majalisar yayin yunkurin gyara dokar masarautun jihar.
Majalisar dokokin jihar Kano za ta yi karatu na uku kan kudirin gyara dokar masarautu da aka kirkiro a mulkin Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf zai sa hannu.
Biyo bayan aniyar majalisar dokkokin jihar Kano na sake fasalin dokar masarautun jihar, Musa Iliysau Kwankwaso ya yi murabus. Ya ce sai 2027 za su kayar da Abba.
Sarkin Kano Muhammad Sanusi Ii
Samu kari