Abin da Ya Faru a Majalisar Kano Inji Wanda Ya Kawo Kudirin Gyara Masarautu

Abin da Ya Faru a Majalisar Kano Inji Wanda Ya Kawo Kudirin Gyara Masarautu

  • Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, Lawan Hussaini Dala ya bayyana abin da ya faru a majalisar a zaman ta na yau
  • Hon. Lawan Hussaini Dala ya bayyana dalilin da ya sa majalisar ta soke masarautu biyar da gwamnatin Ganduje ta kirkira a 2019
  • Shugaban masu rinjayen ne ya fara gabatar da kudurin yin garambawul ga dokar Masarautun Kano da nufin dawo da martar masarauta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Kano, Lawan Hussaini Dala ya bayyana abin da ya faru a majalisar a zaman da ta yi na yau Laraba, 23 ga watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Masu nadi sun isa gidan gwamnati, zasu fara nadin sabon Sarkin Kano

Abin da ya faru a majalisar Kano, Hon. Lawan Dala
Wanda ya kawo kudirin gyara masarautun Kano ya yi magana kan abin da ya faru a majalisa. Hoto: @babarh_ (X)
Asali: Twitter

Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa majalisar jihar Kano ta rushe masarautun da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya kirkira a lokacin mulkinsa.

Abin da ya faru a majalisar Kano

A zantawarsa da BBC Hausa, Hon. Lawan Hussaini Dala ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin da ya faru a zaman majalisa shi ne an soke masarautun Kano guda biyar da aka kirkira, sannan an tabbatar da dawo da tsarin masarauta daya a Kano, wanda aka santa da shi.
"A halin yanzu, sarakuna biyar da aka kirkira ba su da wani matsayi a Kano, da ma kowanne zamani yana zuwa da nasa tsarin, wannan zamanin ya dawo da martabar masarautar Kano."
"Dokar da majalisar Kano ta yi ta shafi duka masarautu biyar, masarautar Kano da muka soke yau sabuwar masarauta ce ba wanda muka sani ta asali ba."

Kara karanta wannan

"Wannan ba cigaba ba ne': Hadimin Buhari ya caccaki Majalisa kan rusa masarautun Kano

- Hon. Lawan Hussaini Dala

Majalisa ta ba Abba wuka da nama

Shugaban masu rinjayen ya yi nuni da cewa majalisa ta ba Gwamna Abba Yusuf wuka da nama domin ya zabi wanda zai zama sabon Sarkin Kano.

Ya ce a halin yanzu wannan dokar na a gaban mai girman gwamnan Kano, inda ake jira ya rattaba hannu kanta tare da tuntubar masu nadin sarki domin gabatar da sunan sabon sarki.

Hon. Lawan Hussaini Dala ya kuma ce majalisar za ta yi zama a gobe Juma'a domin kirkirar dokar sarakuna masu daraja ta biyu a jihar Kano.

Sanusi II ya koma kan kujerar Sarkin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano za ta mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar masarautar Kano bayan da aka tsige shi a shekarar 2019.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa zuwa gobe Juma'a ake sa ran gwamnatin za ta tabbatar da hakan, kuma za a mayar da sarkin ne ba tare da wata tantancewa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel