Sarki Aminu Bayero Ya Bar Kano Yayin da Sanusi II Yake Shirin Komawa Karagar Mulki

Sarki Aminu Bayero Ya Bar Kano Yayin da Sanusi II Yake Shirin Komawa Karagar Mulki

  • Sarki Aminu Ado Bayero (da majalisa ta tsige) ya ziyarci Oba Sikiru Adetona, Awujale na kasar Ijebu a ranar Laraba
  • Hakan na nufin Sarki Aminu Bayero ba ya a cikin Kano lokacin da majalisar jihar ta rusa masarautu biyar na jihar gaba daya
  • A yayin da ake zargin sarakunan Bichi, Rano, Karaye da Gaya su ma ba su cikin Kano yanzu, an ce Sanusi II zai koma karagar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - A yayin da majalisar jihar Kano ta tsige sarakuna biyar na sabbin masarautun da aka kirkira a 2019, an gano cewa Sarki Aminu Ado Bayero ba ya a cikin Kano yanzu haka.

Kara karanta wannan

Dawo-Dawo: An sanar da sabon Sarkin Kano, Sanusi II ya zama sarki a karo na biyu

An ce Sarki Ado Bayero (da majalisa ta tsige) ya ziyarci Oba Sikiru Adetona, Awujale na kasar Ijebu a ranar Laraba.

Sarki Aminu Ado Bayero ya tafi ziyara kasar Ijebu
Sarki Bayero ya bar Kano ana shirin mayar da Sanusi II kan karagar mulki. Hoto: masarautarbichi, sanusilamidoofficial
Asali: Facebook

Bayero da sauran sarakuna sun bar Kano

Bayero tare da hadiman sa sun ziyarci Awujale a Ijebu-Ode domin taya basaraken mai daraja ta daya murnar cika shekaru 90 a duniya, jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, an ce shi ma Alhaji Nasiru Ado Bayero, Sarkin Bichi, wanda kane ne ga Sarkin Kano, ba ya cikin Kano a halin yanzu.

Wata majiya ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa sarkin ya yi tafiya zuwa kasashen waje, amma ba a iya tantance bayanin ba a lokacin gabatar da wannan rahoto.

Haka kuma ba a iya gano inda Sarakunan Rano, Karaye da Gaya suke ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Masu nadi sun isa gidan gwamnati, zasu fara nadin sabon Sarkin Kano

Sanusi II na shirin komawa mulkin Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano na 14, na kan hanyarsa ta komawa kan karagar mulki bayan sauke shi a 2020.

“A halin yanzu Sarki Sanusi yana shirye-shiryen komawar sa kan karagar mulki. Ko da yake ba ya garin a halin yanzu, muna sa ran dawowar sa ranar Juma’a.”

- In ji wata majiyoyi mai tushe.

Wannan kuwa na zuwa ne yayin da majalisar Kano ta rusa masarautu 5 da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkira a 2019.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel