Kwankwaso Ya Ajiye Sarauta Daga Ji Majalisar Kano Za Ta Gyara Dokar Masarautu

Kwankwaso Ya Ajiye Sarauta Daga Ji Majalisar Kano Za Ta Gyara Dokar Masarautu

  • Majalisar dokoin jihar Kano ta amince da kawo gyara kan dokar da ta jawo raba kan masarautar jihar a shekarun baya
  • Biyo bayan lamarin, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ajiye sarauta na sarkin yakin masarautar Karaye a makon yau
  • Sarkin yakin Karaye ya bayyana dalilan yin murabus din tare da yin kira kan babban zabe na shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi murabus daga matsayinsa na sarkin yakin masarautar Karaye kan gyara da majalisar Kano za ta yiwa masarautu.

Musa Iliysa
Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi murabus kan dokar masarautu. Hoto: @Ameenu_Kutama
Asali: Twitter

Sarkin yakin ya bayyana dalilan yin murabus din a wani faifayin bidiyo da northern blog suka wallafa a shafinsu na X.

Kara karanta wannan

Shugaban makaranta ya tsere da kudin jarrabawar WAEC da NECO, ya lula kasar waje

A zamanta na jiya ne majalisar ta amince da kudurin kawo gyara kan dokokin masarautun Kano wanda suka jawo sauke Muhammadu Sanusi II daga sarauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilan murabus din Iliyasu Kwankwaso

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana a faifayin bidiyon cewa zai yi murabus ne domin kare martabar masarautun jihar Kano.

Ya tabbatar da cewa dama ya riga ya yi alkawarin daukar matakin tun kafin zabe kuma lokaci ya yi da zai cika alkawarin.

Kwankwaso zai yi biyayya ga masarautar Kano

Har ila yau Musa Iliyasu Kwankwaso ya jaddada cewa a halin yanzu zai cigaba da nuna goyon baya ga masarautun jihar.

Ya ce dama su suna goyon bayan sarakuna kuma ba zai ja da baya ba. Ya ce wannan matakin da ya dauka yana cikin nuna kishi ga masarautun.

2027: Kiran Iliyasu Kwankwaso ga jama'a

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano ya haifar da marayu da Zawarawa da dama

Har ila yau Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kira ga daukacin al'ummar Kano dangane da babban zaɓen shekarar 2027.

Ya ce matuƙar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta rusa dokar masarautu to dole mutane masu goyon bayan fada su taru su kayar da shi zabe.

Za a dauki mataki kan yan daba a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ce ta ƙuɗiri aniyar magance ayyukan daba da bangar siyasa tsakanin matasan jihar domin samar da ci gaba.

Wannan batu na zuwa ne a lokacin da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi hawa zuwa fadar gwamnatin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel