Muhammadu Sunusi II ya Gaggauta Barin Taro da Jin Labarin Shirin Nada Sabon Sarkin Kano

Muhammadu Sunusi II ya Gaggauta Barin Taro da Jin Labarin Shirin Nada Sabon Sarkin Kano

  • Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sunusi II ya gaggauta ficewa daga taro kan tattalin arziki dake gudana a jihar Rivers jim kadan bayan rushe masarautun Kano
  • Malam Muhammadu Sunusi II ya fice ne bayan bullar labarin cewa gwamnatin Kano za ta mayar da shi karagarsa ta Sarkin Kano mai daraja ta daya
  • Tuni gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya mika sakon taya Malam Muhammadu Sunusu II murnar komawa karagarsa, inda ya ce ra'ayi ne na mutanen Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers-Mai martaba Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sunusi II ya gaggauta barin wani taro da ya halarta a jihar Rivers jim kadan bayan bullar labarin mayar da shi karagarsa.

Kara karanta wannan

Dawo-Dawo: An sanar da sabon Sarkin Kano, Sanusi II ya zama sarki a karo na biyu

Ana tunann Malam Muhammadu Sunusi II ya bar taron ne jim kadan bayan ya kammala gabatar da jawabi kan halin da tattalin arziki ke ciki da zuba jari.

Malam Muhammadu Sunusi II
Malam Muhammadu Sunusu II ya fice daga taro bayan labarin nada shi Sarkin Kano Hoto: Muhammad Sanusi II
Asali: Facebook

Leadership News ta wallafa cewa an kara jibge jami’an tsaro masu rakiyar Sarkin yayin ficewarsa daga taron, wanda ya dauki hankali sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Rivers ya taya Sarki Sunusi murna

Jim kadan bayan rushe sarakunan Kano guda biyar ne gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya taya Malam Muhammadu Sunusi II murnar komawa karagarsa ta Sarkin Kano.

Gwamna Fubara ya taya Sarkin murna ne duk da cewa babu wani jawabi a hukumance daga gwamnatin Kano da ta bayyana hakan.

Kano: Sanusi zai dawo gidan dabo

Pulse Nigeria ta wallafa cewa akwai alamu masu kwari da ke nuna cewa za a mayar da Malam Muhammadu Sunusi na II a matsayin sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Masu nadi sun isa gidan gwamnati, zasu fara nadin sabon Sarkin Kano

A sanarwar da Gwamna Siminalayi Fubara ya fitar, ya ce dawo da Sarki Muhammadu Sunusi II ya zo dai-dai da bukatun al’ummar jihar.

Ya yabawa gwamnatin Kano bisa yin dogon tunanin dawo da Malam Muhammadu Sunusi karagarsa.

Rushe Masarautu: Iyalan Sarki Sunusi sun yaba

A baya mun kawo muku labarin cewa dan Sarkin Kano na 14, Ashraf Sunusi ya bayyana rushe masarautun Kano biyar da majalisar dokokin jihar ta yi da gyara zalunci.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya karawa mahaifinsa lafiya, yayin da ake rade-radin mayar da shi karagarsa ta Sarkin Kano mai daraja ta daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel