Majalisar dattawan Najeriya
Bashir Ahmad, hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bayyana jerin ministocinsa a ranar Talata.
Bola Tinubu ya janye sunayen wasu da ya yi tunanin ba mukamin Minista. Shi dai Akawun majalisa ya ce takarda ba ta shigo hannunsu daga fadar shugaban kasa ba.
Sanatan jihar Abia da ke Kudu maso gabashin Najeriya a majalisar dattawa ta Takawas, Sanata Mao Ohuabunwa, ya rashin mai ɗakinsa, ta rasu a Asibitin Abuja.
Daga cikin yan majalisar dokokin tarayya 400 a Najeriya, 19 ne kacal mata da suka samu damar shiga majalisar dokokin tarayya ta 10 a babban birnin tarayya.
Majalisar dattawa Najeriya ka iya ɗaga tafiya hutun shekara yayin da take dakon saƙo daga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, dangane da Ministocin da zai naɗa.
Majalisar dattawa ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya da ma;aikatanta sun fi kowa kin biyan kudin wutar lantarki kamar yadda rahotanni suka bayyana a makon nan.
A dokar kasa Shugaban kasa da sababbin Gwamnoni ba su isa su wuce Asabar ba tare da sun fitar da mukamai. Idan an aikawa majalisa sunayen, sai a tantance su.
Sanata Victor Umeh mai wakiltar Anambra ta tsakiya, ya musanta raɗe-raɗin cewa sunayen ministocin shugaba Bola Tinubu sun dira majalisar dattawan Najeriya.
A halin da ake ciki, kowa ya kagu ya ji asalin mutanen da Bola Ahmad Tinubu zai nada a matsayin ministocinsa, sai dai har yanzu ba a san su waye ne ba tukuna.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari