Fafatawa Ta Yi Zafi Tsakanin Yari da Akpabio a Tseren Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Fafatawa Ta Yi Zafi Tsakanin Yari da Akpabio a Tseren Zama Shugaban Majalisar Dattawa

  • Zaman majalisar dattawa ya ɗauki ɗumi yayin da ka fara jefa kuri'a kan wanda zai zama shugaban majalisar ta 10
  • Tuni dai aka gabatar da Sanata Godwill Akpabio da Abdul'aziz Yari a matsayin 'yan takara biyu da zasu kara a zauren majalisa da ke Abuja
  • Jam'iyyar APC da kuma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, suna tare da takarar tsohon ministan Neja Delta, Sanata Akpabio

Abuja - Tseren wanda zai zama sabon shugaban majalisar dattawa a majalisa ta 10 ya ɗau zafi da safiyar Talata yayin da Sanatoci suka fara kaɗa kuri'unsu a zauren majalisa da ke Abuja.

Channels tv ta rahoto cewa Sanatocin sun fara kaɗa kuri'a da misalin ƙarfe 8:45 na safiyar Talata, 13 ga watan Yuni kuma ana bin jihohi daki-daki.

Zaben Majalisar Dattawa ya ɗau zafi.
Fafatawa Ta Yi Zafi Tsakanin Yari da Akpabio a Tseren Zama Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: Godwill Akpabio, Abdul'aziz Yari
Asali: Facebook

Yadda aka tsayar da yan takara biyu

Kara karanta wannan

Bayan Doke Yari, Sanata Akpabio Ya Karɓi Rantsuwa, Ya Kama Aiki Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ne ya tsayar da Sanata Godwill Akpabio a matsayin ɗan takarar da ya dace ya zama shugaban majalisar dattawa ta 10.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan haka aka ga Sanata Elisha Abbo daga jihar Adamawa ya miƙe ya tsayar da Sanata Abdul'aziz Yari a matsayin ɗan takara, lamarin da ya so jawo hayaniya tsakanin Sanatoci.

Magatakardan majalisar ya kulle tsayar da 'yan takara bayan hayaniyar da aka fara ta lafa, a cewarsa tunda babu wanda zai sake tsayar da ɗan takara ya ayyana kullewa.

Zaɓe ya ɗauki zafi tsakanin Yari da Akpabio

A halin yanzu tseren ya yi dumi tsakanin Akpabio, tsohon ministan Neja Delta kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, da kuma Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara.

Sanata Akpabio da Sanata Yari duk manyan kusoshi ne a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalilai 5 Da Ka Iya Sa Akpabio Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Sai dai jam'iyyar APC da kuma shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sun ayyana goyon bayansu ga Sanata Akpabio da nufin kawo daidaito a shugabancin ƙasa.

Tun da aka bayyana wannan matsaya, 'yan takara da dama suka hakura suka yi wa jam'iyya biyayya, amma Yari ya tsaya kai da fata cewa kwansutushin ya ba shi damar neman takara.

Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Dokar Bai Wa Dalibai Bashi

A wani rahoton na daban kuma kun ji cewa shugaban ƙasa Tinubu ya rattaɓa hannu a kan kudirin bai wa ɗaliban Najeriya bashin kuɗi su yi karatu.

Wakilin gwamnatin tarayya, Dele Alake, ne ya bayyana haka ga manema labarai na fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin da yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel