Abubuwa 5 da Ya Kamata ku sani Game da Akpabio, Sabon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Abubuwa 5 da Ya Kamata ku sani Game da Akpabio, Sabon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Abuja - A yau Talata, 13 ga watan Yuni ne aka zaɓi Sanata Godswill Akpabio a matsayin sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya.

Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma sanata daga yankin Akwa Ibom ta Arewa maso yamma ne ya lashe zaɓen bayan samun ƙuri’u 63 inda ya doke abokin hamayyarsa, Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, wanda ya samu kuri’u 46.

Babban magatakardar majalisar, Sani Tambuwal ne ya sanar da sakamakon. A cewarsa, sanatoci 107 ne suka kaɗa kuri’un, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Godswill Akpabio ne sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya
An zaɓi Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya. Hoto: Peoples Gazette
Asali: UGC

Akpabio shi ne ɗan takarar da jam’iyyar APC ta tsaida, wanda aka zaɓa a matsayin ɗan ƙasa lamba ta uku, inda Abdulaziz Yari, shi ma a ƙarƙashin jam'iyyar APC, ya ƙalubalance shi.

Ali Ndume daga Borno ne ya tsayar da Akpabio, sannan Adeola Olamilekan daga Ogun ya mara baya.

Kara karanta wannan

Bayan Doke Yari, Sanata Akpabio Ya Karɓi Rantsuwa, Ya Kama Aiki Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi kuwa Yari, Elisha Abbo daga Adamawa ne ya tsayar da shi, sannan Jimoh Ibrahim ya mara baya.

Ga wasu muhimman abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da sabon kakakin Majalisar Dattawan:

1. Rayuwar Akpabio ta baya

Akpabio, wanda ɗan asalin Akwa Ibom ne, an haife shi ne a ranar 9 ga watan Disamba, 1962. Mahaifiyarsa ce ta ci gaba da kula da shi bayan rasuwar mahaifinsa yana ƙarami.

2. Batun Ilmin Akpabio

Akpabio ya halarci makarantar firamare ta Methodist, da ke Ukana, ƙaramar hukumar Essien Udim, da ke jihar Akwa Ibom.

Sannan Akpabio ya wuce zuwa Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Fatakwal, jihar Ribas.

Baya ga haka kuma, Akpabio ya yi digirinsa a Jami’ar Calabar ta jihar Kuros Riba, inda ya samu digiri a fannin shari’a.

3. Ayyuka da sana'o'i da ya gudanar a baya

Kara karanta wannan

Godswill Akpabio Ya Doke Abdulaziz Yari, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Godswill Akpabio ya ɗan yi aiki a matsayin malami kuma abokin aiki a wani kamfanin lauyoyi na Najeriya. Ya kuma yi aiki da kamfanin EMIS Telecoms Limited, wani kamfanin sadarwa a Legas, Najeriya.

A lokacin da yake ke aiki da EMIS, Akpabio ya kai har matsayin manajan darakta na kamfanin.

4. Muƙaman siyasa

A shekarar 2002, Gwamna Obong Victor Attah na jihar Akwa Ibom a lokacin, ya naɗa shi a matsayin Kwamishinan man fetur da albarkatun ƙasa na jihar.

Tsakanin 2002 zuwa 2006, ya yi aiki a matsayin kwamishina a manyan ma'aikatu guda uku:

Ɓangaren mai da albarkatun ƙasa, ma'aikatar harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, da kuma ta filaye da gidaje a shekarar 2006.

Akpabio ya tsaya takarar gwamnan jihar Akwa Ibom a zaɓen fidda gwani, inda ya fafata gami da doke mutane 57 da ke neman tikitin tsayawa takarar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Yaƙin neman zaɓen da ya yi mai taken, “a yi nufin Allah” ya samu goyon bayan jama’a wanda kuma ya taimaka masa wajen zaɓarsa gwamna a 2007. An sake zaɓensa a karo na biyu a 2011.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

A shekarar 2013, an zaɓi Akpabio a matsayin shugaban sabuwar Ƙungiyar Gwamnonin PDP. A shekarar 2015 kuma, ya tsaya takara gami da lashe kujerar Majalisar Dattawa.

Akpabio ya riƙe muƙamin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, wacce a watan Agustan 2018, ya yi murabus a daga kai, sannan kuma ya fice daga PDP zuwa APC.

A watan Yulin shekarar 2019 ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa sunansa, ga Majalisar Dattawa domin tantance shi don a ba shi muƙamin minista.

A watan Yunin 2022, Akpabio ya yi murabus daga mukaminsa na Ministan Harkokin Neja Delta don shiga zaɓen fidda gwani na takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki.

Sai dai daga bisani, a daren da aka gudanar da zaɓen na fidda gwani, ya janye takarar da ga Bola Ahmed Tinubu.

Kwanaki kaɗan bayan kammala zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, ya samu takarar sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, inda ya doke abokin hamayyarsa Emmanuel Enoidem na PDP a babban zaɓe.

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

5. Zargin cin hanci

Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta binciki Akpabio kan zargin karkatar da sama da naira biliyan 100 daga jihar Akwa Ibom a lokacin da yake gwamna tsakanin 2007 zuwa 2015.

Sai dai kuma ba a gabatar da tuhumar gaban kotu ba. ‘Yan sanda sun gurfanar da wani lauya mai suna Leo Ekpenyong a gaban kotu, wanda shi ma ya zargi Akpabio da cin hanci da rashawa, bisa zargin ɓata masa suna.

A watan Mayun 2020 ne ‘yan majalisar wakilai suka gayyaci Akpabio kan tuhumar almundahanar naira biliyan 40.

Akpabio ya karɓi rantsuwar fara aiki

A labarin da Legit.ng ta wallafa, sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya karɓi rantsuwar fara aiki bayan kammala zaɓe wanda ya yi nasara a ciki.

Akpabio shi ne shugaban Majalisar Dattawan na goma a turbar mulkin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel