Yadda Zaben Shugabannin Majalisar Tarayya Yake Gudana a Yau: Kai Tsaye

Yadda Zaben Shugabannin Majalisar Tarayya Yake Gudana a Yau: Kai Tsaye

Abuja - A yau Talata ne za a zabi wadanda za su jagoranci majalisar wakilan tarayya da kuma majalisar dattawa na kasa a babban birnin tarayya Abuja.

Za a so jin labarin wadanda za su shugabanci majalisa ta goma da za a rantsar. Legit.ng Hausa za ta kawo maku da yadda abubuwa su ke gudana yau.

Majalisar Wakilan Tarayya

A majalisar wakilan tarayya, hanya ta kara budewa Hon. Tajuddeen Abbas, akwai yiwuwar zai gwabza ne da Ahmad Wase da su Aminu Sani Jaji a G7.

Daily Trust ta ce Sada Soli Jibia (Katsina) da Miriam Onuoha (Anambra) ba su janye takararsu ba.

Abdulaziz Yari v Akpabio

Rahoton da aka samu daga jaridar The Cable ya nuna Sanata Orji Uzor Kalu da kuma Osita Izunaso za su iya hakura da takararsu a majalisar dattawa.

Ana tunanin Abdulaziz Yari ne babban wanda zai kalubalanci Godswill Akpabio da APC ta tsaida.

A gefe guda, The Nation ta ce an shawo kan manyan Sanatoci irinsu Adamu Aleiro, Danjuma Goje, da Yahaya Abdullahi duk su goyi bayan Akpabio.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce Sani Musa ya fasa takara, ya sallamawa Sanata Jibrin Barau ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Ben Kalu ya zama #2 a Majalisa

Benjamin Kalu daga jihar Abia ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilai. Kalu ya dare kujerar ne ba tare da wata adawa ba.

Premium Times ta ce Jimi Benson mai wakiltar Ikorodu ya tsaida Hon. Kalu, Khadijat Abba-Ibrahim daga Yobe ta mara masa baya.

Mai magana da yawun majalisar ya maye gurbin Ahmad Wase da ya nemi shugabanci.

Abbas ya yi nasara

Tajudeen Abbas ya zama sabon shugaban majalisar wakilai bayan nasararsa a zaben yau.

Daily Trust ta ce Hon. Tajudeen Abbas mai wakiltar mazabar Zariya a jihar Kaduna ya samu kuri'u 353, ya lallasa sauran abokan adawarsa.

Tsohon mataimakin shugaban majalisa, Ahmed Idris Wase, ya samu kuri'u uku rak, haka zalika shi ma Aminu Sani Jaji ya kare da kuri'u uku.

Tajuddeen Abbas ya yi gaba

Gogaggen 'dan majalisar wakiltan tarayya a karkashin jam'iyyar APC, Alhassan Ado Doguwa ya tsaida Hon. Tajuddeen Abbas.

Jaridar Vanguard ta ce Hon. Nnolim Nnaji ya goyi bayan tsaida Abbas. Za a fitar da shugaban majalisar ne ta hanyar zabe a fili.

'Yan takara uku ne a zaben; Tajudeen Abass, Hon. Ahmed Idris Wase da Hon. Aminu Jaji, ana yin zaben ne daga Abia zuwa Zamfara.

A wani bidiyo, an ji wani zababben 'dan majalisar ya ce yana kaunar Ahmad Wase, amma haka nan zai zabi Tajuddeen Abbas.

A halin yanzu kusan duka kuri'un su na tafiya ne ga Tajuddeen Abbas mai wakiltar mazabar Zariya a karkashin jam'iyyar APC.

Akpabio ya yi nasara

Godswill Akpabio ya yi nasara, sakamakon zaben ya tabbatar da shi ne wanda ya fi yawan kuri'un da aka kada.

Tsohon Gwamnan Zamfara ya tashi da kuri’u 46, shi kuwa tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom ya na da kuri'u 63.

Sanatoci sun shiga zabe

A rahoton Vanguard, yanzu Sanatoci sun fara kada kuri'arsu domin zaben wanda zai jagoranci majalisar dattawan Najeriya.

Abdulaziz Yari (Zamfara ta Yamma) zai gwabza da Godswill Akpabio (Akwa Ibom ta Arewa maso yamma), dukkansu a APC.

A halin yanzu Abbo da Ndume za su sa ido domin kirga kuri'un da 'yan takarasu su ka samu bayan an kammala kada kuri'u.

An tsaida 'Yan takara

Daily Trust ta ce Sanata Ali Ndume daga Borno ta Kudu ya tsaida Godswill Akpabio a matsayin ‘dan takaran shugaban majalisar dattawa.

Nan take shi kuma Sanatan Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya tsaida Abdulaziz Yari wanda zai wakilci mazabar Jihar Zamfara ta yamma.

Daga nan ne hayaniya ta kaure a majalisa, Abbo ya fadawa Sanatocin da ba su gamsu da haka ba, su tafi kotu domin su gabatar da korafinsu.

Majalisar Wakilan Tarayya

Da karfe 8:32 aka fara karanto sunayen 'yan majalisar wakilan tarayya da su ka iso zaure domin a rantsar da su a yau.

Bidiyon da aka fitar a Facebook ya nuna ana ta kiran sunan Hon. Pondi Julius G mai wakiltar Burutu a Delta, bai iso ba.

An kira sunan Hon. Iyawe Esosa na jam'iyyar LP, da alama yana cikin zababbun 'yan majalisar da ba su samu karasowa ba.

A cikin 'yan majalisar Gombe, Yaya Bauchi Tongo bai iso ba, haka zalika Adamu Yakubu da Yusuf Galambi daga Jigawa.

Ibrahim Usman Auyo da kuma Bello El-Rufai su na cikin wadanda su ka makara.

Da karfe 9:13 aka shiga karanto sunayen zababbun 'yan majalisar Zamfara bayan karanto 'yan majalisar wakilan Yobe.

Rantsar da Sanatoci

A halin yanzu bidiyo ya fito daga shafin majalisar dattawa na kasa, ya nuna ana shirin rantsar da zababbun 'yan majalisan kasar.

Karfe 8:30 na safiya aka ga Kilakin majalisar tarayya da abokin aikinsa ya na jero sunayen zababbun Sanatocin da suke a halarce.

Da zarar an kira sunan Sanata, zai amsa domin nuna cewa ya na cikin zauren.

Wasu 'Yan Majalisa Sun Iso

Rahoto ya fito daga Tribune cewa tun karfe 6:30 na safiyar yau, ‘yan majalisar wakilai da na dattawa su ka fara hallara majalisar tarayya.

Bayanai sun nuna a cike harabar majalisar ta ke da tsaro yayin da ake shirin yin zabe a yau.

Wani wanda ya ganewa idanunsu, ya shaida cewa manyan motoci hudu sun shigo da ‘yan majalisar, sun biyi ne ta kofar fadar Aso Rock.

An kuma samu karin motoci biyu dauke da zababbun ‘yan majalisar kasar da aka shigo da su ta kofar sakataren gwamnatin tarayya.

An hangi jami’an tsaro su na yi wadannan motoci rakiya domin tabbatar da tsaro.

Online view pixel