Hukumar yan sandan NAjeriya
Biyo bayan samun ingantaccen rahoto, rundunar 'yan sanda ta samu nasar gano wasu makamai da aka boye su a cikin wani buhu a jihar Delta, ana kan neman masu laifin.
Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta yi nasarar cafke wasu matasa biyar kan zargin mallakar bindiga a kauyen Kurmi da ke karamar hukumar Bakori.
Wani matashi mai shekara 19 Muhammad Ibrahim ya kashe budurwarsa saboda ta nemi ya biya naira dubu biyar bayan ta biya masa bukatarsa a 'Bayan Gari' da Bauchi.
Wasu yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba sun yi garkuwa da wata alkaliyar kotu a jihar Akwa Ibom a ranar Litinin, sun kuma kashe dan sanda mai tsaronta.
Jami’an yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ke yin jabun lemuka. SP Benjamin Hundeyin ya saki bidiyon kamfaninsu yayin da ake gudanar da bincike.
Mayakan Boko Haram sun kai sabon hari garin Chibok da ke a jihar Borno, inda suka kashe mutum biyu tare da jikkata wasu da dama. Sun kona gidaje masu yawa.
Rundunar yan sandan jihar Taraba sun samu nasarar sheke wasu yan bindiga mutum uku a wata fafatawa da suka yi. Yan sandan sun kuma ceto mutanen da suka sace.
Kwamitin kudi na majalisar dattawa ya ba rundunar 'yan sanda wa'adin awa 24 ta gurfanar da shugaban hukumar rijistar kamfanoni a gabanta kan kasafin hukumar.
Hukumar EFCC reshen jihar Oyo ta gurfanar da matashi mai suna Olaniyan Gbenga Amos Kan zargin damfarar biliyan daya na zubin hannun jari, an daure shi shekaru 75.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari