Wasu Mata 2 da Karamin Yaro Sun Makale Yayin da Gini Mai Hawa 2 Ya Rufta Kansu a Jihar Legas

Wasu Mata 2 da Karamin Yaro Sun Makale Yayin da Gini Mai Hawa 2 Ya Rufta Kansu a Jihar Legas

  • Akalla mata biyu da wani jariri ake zargin sun makale yayin da wani gini mai hawa biyu ya rufta a yankin Ebute Meta da ke jihar Legas
  • Hukumar kashe gobara da kai daukin gaggawa ta jihar ta ce ta samu nasarar ceto wata mata da ranta, sai dai har yanzu ba ta ceto matan da jaririn ba
  • Legas dai na ci gaba da fuskantar ruftawar gine-gine, inda ko a watan Nuwamba sai da wani gini mai hawa biyu ya rufta tare da kashe wata dattijuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - A safiyar ranar Juma'a ne wani gini mai hawa daya a yankin Ebute Meta da ke jihar Lagos ya ruguje kan mutanen da ke ciki.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Abuja yayin da aka kai hari wata rugar Fulani, an kashe makiyaya biyu

A cikin wata sanarwa daga bakin Margaret Adeseye, daraktar hukumar kashe gobara da kai agajin gaggawa, ta ce mutum uku da suka hada da jarri sun makale a ginin.

Gini ya rufta kan mata biyu da karamin yaro
Gini mai hawa biyu ya rufta kan wasu mata biyu da karamin yaro a jihar Legas. Hoto: @LagosRescue
Asali: Twitter

Adeseye ta ce an samu nasarar kubutar da wata mata da ranta bayan da ginin ya ruguje a kanta, jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce:

"Zuwa yanzu hukumar kashe gobara da kai daukin gaggawa ta fara aikin ceto a wani gini mai lamba 122, titin Herbert Macaulay, Ebute Meta, jihar Lagos, inda ginin mai hawa biyu ya ruguzo.
"Duk da cewa jami'an hukumar sun ceto wata mata da ranta, sai dai akwai mata biyu da wani jariri da suka makale a kasan ginin, ana kokarin ceto su."

The Leadership ta ruwaito cewa wannan rugujewar ginin ya kara yawan adadin gine-ginen da ke ci gaba da ruftawa a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Yar Najeriya ta koka bayan ta bude jakar yar aiki a gida, ta ga abubuwan ban mamaki a ciki

Ko a watan Nuwamba, sai da wata dattijuwa ta mutu bayan wani gini mai hawa biyu ya rufta a titin Oloto da ke Ebute Metta.

A watan Satumba kuwa, rahotanni sun bayyana cewa gini mai sama da dakuna 500 ya rufta a yankin Ketu da ke jihar, inda mutum biyu suka jikkata.

Da fari an yi ginin ne matsayin makaranta amma daga bisani aka mayar da shi gidajen zaman jama'a, inda wani bangare na ginin ya rufta bayan wani ruwan sama mai karfi da aka yi.

Tinubu ya dawo da shirin ciyar da dalibai abinci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umurnin dawo da shirin ciyar da dalibai domin magance yawan daliban da ke gararamba a garuruwan Najeriya.

Gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara kawo shirin ciyarwar amma ya dakatar da shi bayan dogon lokacin da aka dauka ana yin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel