An Daure Matashi Shekaru 75 a Gidan Kaso Kan Zargin Damfarar Biliyan 1, Ya Yi Ta Maza

An Daure Matashi Shekaru 75 a Gidan Kaso Kan Zargin Damfarar Biliyan 1, Ya Yi Ta Maza

  • Wani matashi ya shiga komar EFCC bayan zarginshi da damfarar mutane makudan kudade har biliyan daya
  • Wanda ake zargin mai suna Olaniyan Gbenga Amos ya yi amfani da kamfaninsa ne na zuba hannun jari inda ya damfari jama'a
  • Kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 75 a gidan kaso bayan tuhumarshi kan laifuka 35 a Oyo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Hukumar EFCC reshen jihar Oyo ta gurfanar da wani matashi kan zargin badakalar biliyan daya.

Wanda ake zargin Olaniyan Gbenga Amos an yanke masa hukuncin shekaru 75 a gidan kaso kan damfarar bayin Allah, Legit ta tattaro.

Kotu ta daure matashi shekaru 75 a gidan kaso kan damfarar biliyan daya
Matashin ya damfari mutane da dama har naira biliyan daya. Hoto: @officialEFCC.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani dan sanda ya kashe abokin aikinsa a Rivers, shi ma ya bindige kansa

Alkalin babbar kotun jihar, Bayo Taiwo shi ya yi wannan hukunci a birnin Ibadan a makon da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amos shi ne shugaban kamfanin zuba hannun jarin Detorrid Heritage inda ya damfari mutane da dama kudadensu.

Ana zargin Olaniyan da kamfansa kan tuhume-tuhume guda 35 wanda hukumar EFCC reshen jihar ta gurfanar da su a gaban kotu.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X inda wanda ake zargin ya musanta zargin sa da ake yi.

Mene hukumar EFCC ke cewa?

Sanarwar ta ce:

"Ya damfari mutane da dama da sunan saka musuu a hannun jari wanda kudaden su ka kai naira biliyan daya.
"Amos ya gagara biyansu kudaden da su ka zuba yayin da lokacin biyan ya zo."

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

Lauyan hukumar EFCC, Sunusi Galadanci ya gabatar da shaidu guda shida a gaban kotun.

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, Taiwo ya yanke wa wanda ake zargin shekaru 15 na laifuka biyar daga cikin 15 da ake tuhumarsa.

Ya kuma umarci Amos ya biya dukkan kudaden inda ya ce zai kuma karasa sauran shekarun bayan kammala na farko.

EFCC ta tabbatar da kama tsohon minista

A wani labarin, Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa tsohon ministan wutar lantarki, Olu Ogunloye ya shiga komarta.

Ana zargin Ogunloye da karkatar da naira biliyan shida na aikin wutar lantarki a Mambila da ke jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel