Majalisa Ta Umurci ’Yan Sanda Su Gurfanar da Shugaban Hukumar CAC Cikin Awa 24, Ta Fadi Dalili

Majalisa Ta Umurci ’Yan Sanda Su Gurfanar da Shugaban Hukumar CAC Cikin Awa 24, Ta Fadi Dalili

  • Kwamitin kudi na majalisar dattawa ya ba rundunar 'yan sanda wa'adin awa 24 ta gurfanar da shugaban hukumar rijistar kamfanoni a gabanta
  • Shugaban hukumar, Hussaini Ishaq Magaji ya fara wasan 'yar buya da kwamitin majalisar tun bayan da aka nemi ya kare kasafin kudin hukumar
  • Kwamitin na zargin cewa akwai lauje cikin nadi a kudaden da hukumar CAC ta tara da wanda ta kashe, inda Magaji ya ki bayyana don kare kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar dattawa ta ba shugaban rundunar 'yan sanda umurnin tilasta shugaban hukumar rijistar kamfanoni (CAC), Hussaini Ishaq Magaji ya bayyana gaban majalisar cikin awanni 24.

Shugaban kwamitin kudi na majalisar, Sanata Sani Musa ya yi amfani da karfin ikon da sashen doka na 89 da karamin sashe na 2 ya ba shi na ba da umurnin gurfanar da Magaji.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa likitoci ba sa zama a asabitocin jihar Kogi, CMD ya yi karin bayani

Majalisa ta sa a kamo mata shugaban hukumar CAC
Majalisar dattawa ta ba 'yan sanda awa 24 ta gurfanar mata da shugaban hukumar CAC, Hussaini Ishaq Magaji Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Dalilin da ya sa majalisa ke so a gurfanar da Magaji

Kwamitin na neman Magaji ya yi bayani kan bambance-bambancen da aka samu a kudaden da suka shiga da wadanda suka fita a hukumar rijistar kamfanonin, Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da fari dai kwamitin ya fara zargin hukumar a wani taron kare MTEF/FP, kuma daga lokacin shugaban hukumar CAC ya fara wasan 'yar buya da kwamitin, karo na uku kenan yana haka.

Sanata Musa ya ce wannan raini ne ga kwamitin, yana mai cewa:

"Kana da masu ajiye maka bayanai, kana da kundin bayanan duk abubuwan da hukumar ka ta yi, amma har yanzu ka ki zuwa ka kare kudin da hukumar taka ta samu da wanda ta kashe."

Kwamitin ya yanke shawarar mika lamarin ga shugaban rundunar 'yan sanda na kasa don tilasta Magaji bayyana gaban kwamitin a ranar Alhamis ba tare da fashi ba.

Kara karanta wannan

Hutun Kirsimeti: Tinubu ya zabtare rabin farashin ababen hawa, tafiya a jirgin kasa kyauta ne

inubu ya zabtare farashin ababen hawa saboda bikin Kirsimeti

A wani labarin, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabtare farashin motocin haya da kaso 50% a tafiye-tafiyen jiha zuwa jiha don bikin Kirsimeti da sabuwar shekara

Haka zalika, shugaban kasar ya ba da umurnin cire kudin hawan jirgin kasa, wanda ke nufin matafiya za su hau jirgin kasa kyauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel