Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Babban Mai Sarautar Gargajiya, Sun Sace Matarsa, Dansa da Wasu Mutum 8

Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Babban Mai Sarautar Gargajiya, Sun Sace Matarsa, Dansa da Wasu Mutum 8

  • Masu garkuwa sun hallaka dagajin Garin Modibbo inda su ka sace matarsa da dansa guda daya a karamar hukumar Ardo-Kola da ke jihar Taraba
  • Marigayin, Alhaji Muhammadu ya rasa ransa ne bayan maharan sun kai mummunan hari a jiya Litinin 30 ga watan Oktoba
  • Shugaban karamar hukumar, Dalhatu Kawo ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ya kai rahoton ga gwamnatin jihar don daukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - ‘Yan bindiga sun hallaka mai sarautar gargajiya na Garin Modibbo, Alhaji Muhammadu yayin da su ka sace matarsa da kuma dansa a jihar Taraba.

Ana zargin ma su garkuwan da kashe mai sarautar gargajiyan bayan sun kai farmaki a ranar Litinin 30 ga watan Oktoba a kauyen da ke karamar hukumar Ardo-Kola.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya ba da umarnin tantance karin mutane 147 don auren gata, ya bayyana matakin gaba

'Yan bindiga sun hallaka mai sarautar gargajiya, sun sace iyalinsa a Taraba
Mutane Sun Dimauce Bayan ’Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Mai Sarautar Gargajiya a Taraba. Hoto: Gov. Kefas.
Asali: Twitter

Yaushe aka hallaka Dagacin a Taraba?

Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun kai hari kauyen da misalin karfe 11:30 na dare a jiya Litinin 30 ga watan Oktoba tare da sace matarsa da kuma dansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ‘yan bindigan sun dauke wasu mutane hudu a kauyen kafin daga bisani su shiga kauyukan da ke kusa da sace wasu hudu har da mai shayarwa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san dalilin kisan dagajin garin ba da ‘yan bindigan su ka yi.

Wane mataki aka dauka kan harin a Taraba?

Sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar cewa marigayin na goyon bayan matasa don yaki da masu garkuwa, Legit ta tattaro.

Mafarauta karkashin jagorancin shugabansu, Dantala Adamu sun bazama dazuka da kan duwatsu don kwato wadanda aka sacen.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke daliban firamare 2 da cinna wa makarantarsu wuta, an bayyana yadda abin ya faru

Shugaban karamar hukumar Ardo-Kola, Dalhatu Kawu a tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ya kai rahoton ga gwamnatin jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai ba da cikakken bayani ba kan lamarin.

Sojoji sun hallaka kwamandan 'yan bindiga a Kebbi

A wani labarin, Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka kwamnadan ‘yan bindiga Mainasara a jihar Kebbi.

Rundunar ta samu wannan nasara ne bayan kai farmaki kan ‘yan bindigan a karamar hukumar Dango Wasagu a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel