Yan Bindigar da Suka Sace Ma’aikacin CBN da Wasu 2 Suna Neman N10m Kudin Fansa

Yan Bindigar da Suka Sace Ma’aikacin CBN da Wasu 2 Suna Neman N10m Kudin Fansa

  • Tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne, wadanda suka sace ma'aikacin CBN da wasu biyu sun yi tuntuba
  • Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya naira miliyan 10 a matsayin kudin fansar Isaac Bature Gbaja da sauran mutum biyu da suka sace
  • Sai dai kuma, har yanzu ba a samu jin ta bakin rundunar yan sandan jihar ba a kan wannan al'amari

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Yan bindigar da suka yi garkuwa da Isaac Bature Gbaja, mataimakin manajan babban bankin Najeriya (CBN) reshen Lafia a daren ranar Litinin, sun bukaci a biya naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, baya ga ma'aikacin CBN din, yan bindigar sun kuma sace wasu mutane biyu da ba a san sunayensu ba har a lokacin kawo wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Mahara sun bukaci miliyan 53 kudin fansar malamin addini da wasu mutum 2 a jihar Arewa

Yan bindiga na neman kudin fansar ma'aikacin CBN da wasu biyu
Yan Bindigar da Suka Sace Ma’aikacin CBN da Wasu 2 Suna Neman N10m Kudin Fansa Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Wani makusancin ma'aikacin CBN din wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya fada ma jaridar cewa an sace Gbaja ne tare da sauran mutanen da misalin karfe 8:00 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cewa lamarin ya afku ne a wajen cin abincin matarsa kusa da MACFES Royal Suites, hanyar Kwandere, Tudun Gwandara, Lafia, jihar Nasarawa.

Jaridar National Accord ta rahoto cewa ma'aikacin CBN din na hutawa tare da kwastamomin matarsa lokacin da wasu yan bindiga uku suka farmaki wajen sanye da safa a fuskarsu sannan suka yi awon gaba da su.

Lamarin na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan wani kansila da yan bindiga suka sace a karamar hukumar Lafia ya samu yanci.

Martanin yan sandan Nasarawa

Har yanzu ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Nasarawa, DSP Rahman Nansel, ba saboda baya amsa waya kuma bai amsa sakon tes da aka aike zuwa layin wayarsa ba.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya gamu da babban cikas a jihar Ƙaduna yayin da ma'aikata suka rabu gida biyu

Dan shekara 9 ya sace yarinya a Bauchi

A wani labarin, mun ji cewa kwamishiniyar harkokin mata da cigaban ƙananan yara, Hajara Gidado, ta bayyana yadda wani yaro Almajiri ɗan shekara tara, wanda aka ɓoye sunansa, ya sace wata yarinya ƴar shekara biyar a gidan mahaifinta.

Ta bayyana hakan ne a wajen bude taron horar da malaman Tsangaya da na Islamiyya na kwanaki biyu a ɗakin taro na Sa’ad Abubakar da ke Hajj Camp a Bauchi, cewar rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel