Manyan Labarai A Yau
Majalisar dokokin jihar Kwara ta sake zaɓar Engr. Yakubu Salihu-Danladi a matsayin kakakinta a karo na biyu. Yakubu matashi ne sharaf mai shekara 38 a duniya.
Rahotanni sun tabbatar da ƴan daba sun sari wani ɗalibin jami'ar Sa'adu Zungur da ke a Gadau a jihar Bauchi bayan gardamar ƙwallon ƙafa ta rikiɗe ta koma faɗa
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta zaɓi Bilyaminu Moriki a matsayin saɓon kakakinta. Hon. Bilyaminu ya samu hawa kan kujerar shugabancin ba tare da hamayya ba.
Sanata Barau Jibrin ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa a zaɓen da aka gudanar ranar 13 ga watan Yuni. Gogaggen ɗan siyasan ya fito daga jihar Kano.
Rahotanni sun tabbatar da aukuwar wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a wani ƙauye cikin jihar Kwara. Jirgin mai ɗauke da mutum 100 ya kife ne ana cikin tafiya.
Wata matar aure ta bayyana halin tsaka mai wuya da ta samu kanta a ciki yanzu. Tace ƴaƴanta 4 surikinta ne mahaifin su kuma mijinta bai sani ba. Ta rasa abin yi
Rahotanni sun tabbatar da dangantaka na ƙara tsami a tsakanin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da mataimakinsa Orimisan Aiyedatiwa kan ragamar mulkin jihar.
Bangaren Sanata Abdulaziz Yari, ɗaya daga cikin na gaba-gaba a takarar shugabancin majalisar dattawa, ya musanta zargin yin amfani da kudi domin siye sanatoci.
Kashim Shettima ya bayyana cewa a shirye yake ya ɗuka ƙasa kan guiwoyinsa domin ya roƙi zaɓaɓbun sanatoci su zaɓi Godswill Akpabio shugaban majalisar dattawa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari