Majalisa Ta 10: Bangaren Sanata Abdulaziz Yari Ya Musanta Siye Zababbun Sanatoci Da Kudi

Majalisa Ta 10: Bangaren Sanata Abdulaziz Yari Ya Musanta Siye Zababbun Sanatoci Da Kudi

  • Takarar neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10 na ƙara ɗaukar ɗumi inda ake dab da raba gardama kan wanda zai ɗare kan kujerar
  • Sanata Godwill Akpabio Sanata Abdulaziz Yari su ne akan gaba-gaba wajen takarar neman shugabancin majalisar
  • Akwai zarge-zargen cewa Yari ya fara siye zaɓaɓɓun sanatocin da kuɗaɗe, zargin da ɓangaren tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya fito ya musanta

FCT, Abuja - Biyo bayan rahotannin cewa zaɓaɓɓun sanatoci sun fara siyar da ƙuri'unsu kan daloli masu yawa, ɓangaren Sanata Abdulaziz Yari ya musanta cewa suna da hannu a ciki.

Rahotannin sun bayyana cewa zaɓaɓɓun sanatocin sun fara siyar da ƙuri'unsu akan maƙudan kuɗaɗe har $5000 zuwa $10,000 da abinda ya fi haka.

Yari ya musanta zargin yin amfani da kudi
Abdulaziz Yari da Godswill Akpabio Hoto: Abdulaziz Yari, Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Kamar yadda Daily Independent ta rahoto, Akapabio ya kira taro da zaɓaɓɓun sanatoci ranar Asabar, 10 ga watan Yuni a otal ɗin Transcorp Hilton da ke a birnin tarayya Abuja

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Kashim Shettima Ya Bayyana Muhimmin Abu 1 Da Zai Yi Wa Zababbun Sanatoci Domin Su Zabi Akpabio

A cewar rahotannin taron bai samu halartar zaɓaɓɓun sanatoci da yawa ba saboda sun sauya sheƙa zuwa wajen Abdulaziz Yari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bangaren Yari ya musanta amfani da kuɗi

Da yake martani kan zargin siye zaɓaɓɓun sanatocin da kuɗi, wani zaɓaɓɓen Sanata na ɓangaren Yari ya bayyana hakan a matsayin abin dariya.

A kalamansa:

"Ba ƙanshin gaskiya ƙarya ce kawai tsantsagwaronta, cin fuska ne da rashin sanin yakamata da ƙoƙarin ɓata suna wanda bai dace ba ga wanda duk yake son zama shugaban waje mai muhimmanci kamar majalisar dattawa."

Dalilin sanatocin na barin Akpabio

Haka kuma wani zaɓaɓɓen sanata daga ɓangaren Akpabio, ya bayyana zargin a matsayin ƙage ne kawai wanda baya da tushe ballantana makama.

Ya bayyana cewa zaɓaɓɓun sanatocin sun koma wajen Yari ne ba domin an basu kuɗi ba, face sai don rashin ƙwarewar Akpabio da kuma takun saƙar da ya taɓa yi da majalisar a lokacin da yake muƙamin minista.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Mayar Da Atiku Abin Tsokana, Ya Yi Masa Shagube a Bainar Jama'a

"Na bar Sanata Akpabio ne bayan na fahimci cewa baya da ƙwarewa da ƙimar mutunta majalisa." A cewarsa
"Da yawa daga cikinmu mun fahimci hakan. Wannan ra'ayinmu ne kuma muna da ƴancin yin zaɓin ƙashin kan mu."

Shettima Zai Nemi Alfarma Wajen Sanatoci

A wani labarin, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana shirinsa na neman goyon bayan sanatoci su zaɓi Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10.

Shettima ya bayyana cewa a shirye yake ya ɗuka ƙaasa kan gwiwoyinsa domin ya nemi alfarma a wajen sanatocin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel