Tirkashi: Matar Auren Da Ta Haifawa Surikinta Yara 4 Ta Koka, Tace Mijinta Baya Da Masaniya

Tirkashi: Matar Auren Da Ta Haifawa Surikinta Yara 4 Ta Koka, Tace Mijinta Baya Da Masaniya

  • Wani rubutu da ya karaɗe manhajar Twitter na wata matar aure da taci amanar mijinta ya tayar da ƙura
  • Matar wacce ta sakaya sunan ta a saƙon da ta turo ta bayyana cewa sun biyawa juna buƙata ita da surikinta
  • Inda abin ya ƙara muni shine dukkanin ƴaƴan ta guda huɗu ba ƴaƴan mijinta bane, ƴaƴan surikinta ne

Wani rubutu a shafin @CapitalFMUganda a manhajar Twitter, ya sanya mutane da dama fusata da jin kunya.

Wata matar aure ce dai ta bayyana labarin ta wanda ya kasance ya zama abin takaici matuƙa.

Matar ta bayyana cewa bayan sun kwashe lokaci tare da mijinta ta gano cewa ba zai iya haihuwa ba.

Matar Aure
Tirkashi: Matar Auren Da Ta Haifawa Surikinta Yara 4 Ta Koka, Tace Mijinta Baya Da Masaniya Hoto: FG Trade, Getty Images
Asali: Getty Images

Surikinta shine ya gaya mata cewa mijinta ba zai iya yiwa wata mace ciki ba. Sai ya bata shawarar domin rufawa mijinta asiri, shi (surikin na ta) sai ya kwanta da ita domin ta samu juna biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba tare da yin shawara da mijinta ba ta amince suka riƙa cin amanar sa da mahaifin sa. Ta samu juna biyu inda har ta haifi yara huɗu tare da surikin na ta waɗanda ta bar su a matsayin ƴaƴan mijinta.

Sati biyu da suka gabata, surikin nata ya mutu, sai kwatsam cin amanar da tayi wacce a baya take ganin daidai ne, ta riƙa damun ta, inda take jin cewa bata kyauta ba.

Yanzu ta rasa mafita tana tunanin gayawa mijinta gaskiya dangane da haƙiƙanin mahaifin yaran.

Rubutun na cewa:

"Mun kwashe shekaru takwas tare da mijina. Muna da yara huɗu amma babu ko ɗaya na shi a cikin su. Ƴaƴan mahaifin sa ne, surikina. Mijina yana matuƙar son ƴaƴa amma mahaifin sa ya san ba zai iya haihuwa ba. Sai ya sanya muka ƙulla yarjejeniya yadda ɗan sa ba zai kunyata ba."

"Mahaifin sa ya mutu mako biyu da suka wuce sannan yanzu wannan sirrin yana damuna. Shin na gaya masa gaskiya ko na yi shiru?"

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

@Edward Amanyire ya rubuta:

"Ba za a yarda da abinda tace ba saboda gwajin DNA zai yi daidai da na mijin tunda yaran ƙannen sa ne. Idan wannan gaskiyar ta fito ta ya za a iya tantancewa. Mahaifin ya mutu da gaskiyar, ba za a yarda da ita ba tunda wannan gaskiyar za ta yi wahalar tantancewa"

Rahumatk ta rubuta:

"Kiyi shiru kawai kasita duk ƴan tsatso ɗaya ne mukwano, kada ki kunyata mijinki.. kada ki manta kin yi alƙawari Kati silika mpaka kufa."

@DrBluetooth Ug ya rubuta:

"Shin kin fahimci cewa ƴaƴan surikin ki surikan ki ne? Kenan ƴaƴanki za su kiraki surika kuma ke surikar mijinki ce kuma matar mahaifin sa, sannan yanzu kin zama bazawara, ta wani fannin ƴaƴan ki sun zama marayu, sannan suna da uba da jika ɗaya daga ciki ya mutu."

Bayan Shekara 8 Suna Zaman Dadiro, Wasu Masoya Sun Rabu Da Juna

A wani labarin na daban kuma, wasu masoya sun raba gari bayan kwashe shekara 8 suna zaman dadiro.

A yayin rabuwar su, saurayin ya yiwa budurwar wani abu wanda ya sosa mata rai matuƙa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel