Emefiele Ya Shafe Kwana Na Biyar a Hannun DSS, Da Wasu Abubuwan Da Yakamata Ku Sani

Emefiele Ya Shafe Kwana Na Biyar a Hannun DSS, Da Wasu Abubuwan Da Yakamata Ku Sani

  • Yanzu dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya shafe kwana biyar a tsare a hannun DSS kuma babu alamun sako shi
  • Hakan ya faru ne saboda rundunar ƴan sandan farin kayan ta ƙi bayyana sakamakon bincikenta kan Emefiele tun bayan da ta cafke shi
  • A baya Emefiele ya samu matsala tsakanin shi da DSS inda har umarnin kotu ta nemi domin cafke shi bisa zargin ɗaukar nauyin ta'addanci

Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, ya shafe kwanaki biyar a tsare a hannun rundunar ƴan sandan farin kaya ta DSS, inda rundunar ba ta bayar da cikakkun bayanai ba kan cafke shi.

Emefiele ya shafe kwana biyar a hannun DSS
Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan CBN Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

A cewar rahoton The Guardian, yau Laraba, 14 ga watan Yuni, Emefiele yake cika kwanaki biyar a tsare a hannun DSS bayan sun cafke shi biyo bayan dakatarwar da shugaba Tinubu ya yi masa a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

DSS ta Raba Emefiele da Fasfon Fita Kasar Waje, Za a Binciki Ofishi da Gidajensa

Dangantakar Emefiele da DSS a baya

Kafin ya shiga hannun DSS, dakataccen gwamnan na CBN yana da dangantaka mai tsami tsakaninsa da rundunar ƴan sandan farin kayan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A shekarar da ta gabata, DSS ta zargi Emefiele da aikata laifuka da dama inda har a ɓoye ta nemi umarnin kotu domin ta cafke shi, bisa zargin ɗaukar nauyin ta'addanci da wasu laifukan.

Sai dai, babbar kotun tarayyar mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta yi fatali da buƙatar DSS saboda hukumar ta kasa kawo ƙwararan hujjoji da za su sanya kotun ta bayar da umarnin.

Emefiele ya so tsayawa takara a inuwar jam'iyyar APC

An caccaki Emefiele a shekarar da ta gabata saboda ya yi ƙoƙarin tsunduma cikin siyasa wajen shiga takarar zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Emefiele: Jerin Zarge-Zargen Da Ake Yi Wa Dakataccen Gwamnan CBN Yayin da DSS Ta Yi Sabon Yunkuri

A halin da ake ciki a yanzu, babu wata alamar cewa za a sako Emefiele. Hukumar DSS har yanzu ta ƙi bayyana sakamakon binciken da take yi akan dakataccen gwamnan babban bankin.

Naira Ta Yi Daraja Bayan Dakatar Da Emefiele

Rahoto ya zo kan yadda darajar naira ta ƙara farfaɗowa biyo bayan dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da Shugaba Tinubu ya yi.

Darajar naira ta ƙaru akan dalar Amurka inda yanzu ta koma N754/$1 a maimakon N767/$1 da take a baya kafin a dakatar da Emefiele.

Asali: Legit.ng

Online view pixel