"Na Gaji Da Zama Babu Aure": Shahararriyar 'Ƴar TikTok Ummi Darling Na Neman Mijin Aure

"Na Gaji Da Zama Babu Aure": Shahararriyar 'Ƴar TikTok Ummi Darling Na Neman Mijin Aure

  • Shahararriyar jarumar ds ta yi fice wajen tiƙar rawa a TikTok, ta bayyana cewa rashin mijin aure na ci mata tuwo a ƙwarya
  • Saudat Shehu wacce aka fi sani da Ummi Darling tace ta gaji da zaman da ta ke yi hakanan babu mijin aure inda ta ƙosa ta shiga daga ciki
  • Shahararriyar ƴar TikTok ta bayyana cewa a shirye ta ke ta tuba daga TikTok domin ta samu mijin da za su yi aure

Shaharrarriyar ƴar TikTok, Saudat Shehu wacce aka fi sani da Ummi Darling, ta bayyana cewa ta gaji da zama hakanan babu miji sannan a shirye ta ke ta yi zaman aure a matsayin kamilar matar aure.

Ƴar TikTok ɗin wacce ke da kwalin difloma daga jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria, ta yi fice ne a dalilin bidiyoyin rawarta.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Da Ke Gab Da Yin Aure Ya Rasa Ransa Sakamakon Nutsewa A Ruwa A Enugu

Ummi Darling ta shirya barin TikTok domin yin aure
Rashin miji na damun Ummi Darling Hoto: @ummiee_darling
Asali: TikTok

A cikin wani bidiyo Ummi Darling ta bayyana cewa tana son ta watsar da harkar TikTok ta yi aure, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Ta shirya tuba daga rawa a TikTok

A kalamanta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina son na tuba na daina TikTiok saboda ina son na yi aure. Na gaji da zama babu mijin aure. Duk da cewa a yanzu bani da saurayi saboda ban yarda da soyayyar ƙarya ba, sannan ina son na yi soyayya da mutum mai hankali ba yaro ba."
"Ina son namiji wanda zai ɗauki nauyin dukkanin ɗawainiya ta a matsayin matarsa tare da sauke dukkanin nauyin da ya rataya a wuyansa na miji."

Ummi darling ta yi fice sosai a TikTok shekara biyu da suka gabata saboda baiwar tiƙar rawar da ta ke da ita.

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

Tana kiran kanta a matsayin sarauniya wacce ta ke yin rawa kawai a waƙoƙin soyayya duk da a lokuta da dama ta sha bayyana cewa ba ta yarda da soyayya ba.

'Yar TikTok Na Son Yin Wuff Da Kwamandan Hisbah

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa shahararryar mai rawa a TikTok ƴar jihar Kano, ta bayyana aniyarta na son auren babban kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina.

Hafsat Fagge ta bayyana cewa a shirye ta ke ta yi na'am da batun aure daga wajen babban kwamandan Hisbah na jihar Kano, idan har yana da ra'ayin aurenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel