Manyan Labarai A Yau
Wani magidanci ɗan Najeriya na duba yiwuwar rabuwa da ita saboda ya dai na jin son ta a zuciyarsa. Ya bayyana cewa yanzu kallon ta yake yi kamar ƴar'uwarsa.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya zama sabon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa a ranar Alhamis, 3 ga watan Agustan 2023.
Allah ya yi wa tsohuwar babbar mai shari'a ta jihar Bayelsa, Kate Abiri, rasuwa ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, 2023 bayan fama da jinya ta gajeren lokaci.
Majalisar zartaswa ta ƙasa (NEC) ta jam'iyyar APC a ranar Alhamis, 3 ga watan Agustan 2023, ta zaɓi Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.
Uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Oluremi Tinubu da uwargidan mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, Nana Shettima sun ziyarci Buhari a Daura.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), na gudanar da taron majalisar zartaswar jam'iyyar a Abuja.
Ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun sake kai wani mummunan hari a yankin tafkin Chadi, inda suka halaka masunta masu yawan gaske ta hanyar yi musu yankan rago.
Hedikwatar hukumar tsaron ta ƙasa ta fito ta yi magana kan batun cewa Shugaba Bola Tinubu, ya shirya amfani da ƙarfin soja kan sojojin juyin mulki na Nijar.
Kungiyoyin ƙwadago na ƙasar nan sun dakatar da shiga yajin aikin da su ke shirin farawa a faɗin ƙasar nan domin nuna adawa da tsare-tsaren gwamnati masu tsauri.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari