“Ya Kashe Miliyan 10.7”: Wani Mutum Ya Mayar Da Kansa Kare, Ya Fito Bainar Jama’a

“Ya Kashe Miliyan 10.7”: Wani Mutum Ya Mayar Da Kansa Kare, Ya Fito Bainar Jama’a

  • Wani mutum ya sauya kansa zuwa wani kare da taimakon wani kaya da yasa shi komawa tamkar cikakken kare na gaske
  • Mutumin mai suna Toco ya samu wani kamfanin kasar Japan ya kera masa rigar karen kan kudi naira miliyan 10.7
  • Karnuka da mutane sun cika da mamaki bayan sun ga yanayin girmansa da yadda yake wasa a lokacin da ya fito bainar jama'a

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutumin kasar Japan ya kashe kudi har naira miliyan 10.7 wajen siyar rigar kare wanda ya sanya shi kama da karen gaske.

Mutumin mai suna Toco ya ce a kodayaushe yana son ya ga ya zama tamkar wani dabba kuma cewa wannan rigar karen ya taimaka masa wajen ganin mafarkinsa ya zama gaskiya.

Wani mutum ya saka rigar kare
“Ya Kashe Miliyan 10.7”: Wani Mutum Ya Mayar Da Knasa Kare, Ya Fito Bainar Jama’a Hoto: YouTube/I Want to Be an Animal.
Asali: Youtube

A yanzu kafar Toco na Youtube yana da mutane fiye da 47,000 da suke bibiyarsa. A daya daga cikin bidiyon, Toco ya bayyana karara cewa zama tamkar wani kare mafarki ne da ya zama gaskiya.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Tsere A Gidan Kaso Watanni 4 Kafin Wa'adinsa, Ya Shiga Tasku Bayan Kama Shi Da Kara Masa Shekaru 40

Ya rubuta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sunana Toco, ina so in zama dabba kuma na zama kare. Wannan kafar za ta kawo maku bidiyoyin kare na daban a cikinsu! A wannan lokacin, na samu damar cika mafarkina da na dade ina yinsa tun ina dan karamin yaro; zama kare da yin tattaki a waje!"

Mutane sun yi martani

A wani bidiyo wanda tuni ya yadu kuma ya samu mutum fiye da miliyan 7 da suka kalle shi, Toco ya fito bainar jama'a a karon farko.

Mutane da karnuka masu kamanni sun cika da mamaki lokacin da suka ga Toco yana gaisawa da daga masu hannu yayin da yake kwance.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin mutane

@genevahart6952 ta ce:

"Hatta su kansu karnukan sun san cewa akwai matsala."

@adrianmusliu4409 ya ce:

"Wannan shi ne abun ban mamaki da hauka da na taba gani."

Kara karanta wannan

“Albashina Na Farko a Canada”: Matashi Dan Najeriya Da Ya Koma Turai Da Zama Ya Siya Hadaddiyar Mota

Abokan ango sun tabbatar da ko bakinsa yana wari kafin ya sumbaci amaryarsa a wajen biki

A wani labari na daban, wani mutumi ya nuna yar dirama da abokansa suka shirya a lokacin da zai sumbaci amaryarsa a ranar aurensu. Yayin da shi (@y0ung.15) ya bude fuskar matar, sai daya daga cikin abokansa ya yi masa gyaran fuska.

Wani abokin ango kuma ya duba ko yana kamshi kafin ya ba shi turaren jiki ya fesa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel